Nigerian news All categories All tags
Bamu razana da tsayawar Buhari takara ba - Magoya bayan Atiku

Bamu razana da tsayawar Buhari takara ba - Magoya bayan Atiku

- Kungiyar magoya bayan Atiku sunce ba wani sabon abun mamaki bane don Buhari yace zai tsaya takara a karo na biyu

- Shugaban kungiyar Ferguson Okpala yace basu damu ba saboda hakan zai karawa matasa karfin gwiwa na tsayawa takarar

- Yace idan har jam’iyyar adawa naso tayi nasara a zabe na gaba dolene su tsayar da dan takara na kirki

Kungiyar magoya bayan Atiku Abubakar, mai lakabi da Atiku Grassroots Ambassadors, sunce ba wani sabon abun mamaki bane don Buhari yace zai tsaya takara a karo na biyu, sun bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya hakane a ranar 10 ga watan Afirilu, 2018.

Shugaban kungiyar Ferguson Okpala yace basu damu ba saboda hakan zai karawa matasa karfin gwiwa na tsayawa takarar, ya fada hakane lokacin da yake zantawa da NAN, a garin Awka, a ranar Talata.

Yace idan har jam’iyyar adawa naso tayi nasara a zabe na gaba dolene su tsayar da dan takara na kirki.

Bamu razana da tsayawar Buhari takara ba - Magoya bayan Atiku

Bamu razana da tsayawar Buhari takara ba - Magoya bayan Atiku

“Garemu ribace tsayawar Buhari takara saboda hakkinsa ne, saoba haka yana da damar yin abunda ransa keso, saboda haka a barshi.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya nada lauyan Zakzaky a matsayin kwamisinan INEC

“Amma mu jindadi ne garemu tinda munsan daya daga cikin ‘yan adawarmu. ‘Yan Najeriya dai suna da wayon sanin yanda zasu zabi wanda suke so.

“Abunda kawai muke bukata shine jam’iyyar PDP tayi abunda ya dace, ta bawa Atiku tikitin tsayawa a matsayin dan takarar jam’iyyar, saboda shine kadai ya cancanta kuma ya kai matsayin fuskantar Buhari,” Inji su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel