Nigerian news All categories All tags
Mutan garinsu Ben-Bruce sun fara juyawa salon siyasar sa baya

Mutan garinsu Ben-Bruce sun fara juyawa salon siyasar sa baya

- Rahotanni sun bayyana cewa al'ummar yankin da Sanata Ben Bruce ke wakilta sunce bai cancanci ya zarce ba

- Al'ummar mazabar nashi suna zargin sa da rashin tabuka wani abin kwarai a Majalisar

- Sun shawarci Sanata ben Bruce ya koma sana'arsa na talabijin

A ranar Talata ne al'ummar yankin Gabashin Bayelsa wato mazabar Sanata Ben Bruce suka bayar da sanarwar cewa Sanatan bai cancani ya zarce a kujerarsa ba a zaben 2019 mai zuwa.

Jaridar the Nation ta ruwaito cewa al'ummar mazaban sunyi ikirarin cewa Sanatan bai wakilce su kamar yadda ya dace ba hakan yasa suka shawarce shi ya manta da siyasa ya koma sana'arsa ta harkar talabijin da nishadantarwa.

Mutan garinsu Ben-Bruce sun fara juya masa salon siyasar sa baya

Mutan garinsu Ben-Bruce sun fara juya masa salon siyasar sa baya

DUBA WANNAN: Gwamna Ortom ya bawa 'yan gudun hijira shawara yadda zasu kare kansu

Legit.ng ta gano cewa mutanen jihar sun goyi bayan Nimi Barigha-Amange wanda ya wakilci yankin a majalisa ta shida data gabata. Sun sanarwa da cewa a zamanin da Amange yake wakiltan yankin, sun sami ingantaciyar wakilici.

A karshen wata taron masu ruwa da tsaki da ya samu hallarcin mutane kamar su John Thatcher, David Obodor, Afen Bright, Wilson Abel, Oscar Egberi, Jeff Afagha, Angela Ikokote, Rev. Ranami Afagha, Atim Atim-King da sauransu, duk sun amince cewa Amange ne ya dace ya wakilci yankin.

A jawabin da daya daga cikin mahalarta taron, Wilson Abel yayi, yayi kira ga al'ummar yankin suyi watsi da rashin jagoranci na gari, talauci, rashin iya mulki da wahalhalu. Ya kara da cewa mazabar bazata amince da mutanen da basu san abinda al'ummar mazaban ke ciki ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel