Nigerian news All categories All tags
Buhari: Ba lallai ne shekaru ya zamo kalubale ba a zaben 2019 – Inji Onaiyekan

Buhari: Ba lallai ne shekaru ya zamo kalubale ba a zaben 2019 – Inji Onaiyekan

Babban limamin cocin Abuja Diocese John Cardinal Onaiyekan ya bayyana cewa ba lallai bane shekaru ya zamo kalubale ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa.

Ya bayyana cewa abun da ke da muhimmanci ga masu neman shugabanci shine kula da sauran mutane tare da yiwa mutane aiki da sunan Allah.

Koda dai yace akwai bukatar a ba matasa damar shugabanci, ya nuna danasani daga abubuwan da suka gudana a baya, matasan da aka zaba basu tabuka komai ba.

Buhari: Ba lallai ne shekaru ya zamo kalubale ba a zaben 2019 – Inji Onaiyekan

Buhari: Ba lallai ne shekaru ya zamo kalubale ba a zaben 2019 – Inji Onaiyekan

KU KARANTA KUMA: Sanatan Kaduna yana neman daukowa Shugaban Jam’iyyar APC Oyegun aiki

Limamin wanda yayi Magana a taron kaddamar da littafin tarihin tsohon ministan harkokin waje, Cif Mathew Mbu yace ya zama dole masu neman zabe su bayar da hujjoji masu karfi.

A halin da ake ciki rikicin cikin gidan da ake fama da shi a Jam’iyyar APC mai mulki yana nema yayi kamari. Yanzu haka dai ku na da labari cewa Shugaban kasa Buhari da wasu sun nemi ka da su John Odigie-Oyegun su cigaba da zama a kujerun su.

Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya yabawa wannan mataki da Shugaba Buhari da irin su Bola Tinubu su ka dauka. Sanatan yace ya kamata kuma a binciki irin badakalar da John Oyegun da Majalisar sa su ka tafka a ofis.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel