Nigerian news All categories All tags
Gwamna Ortom ya bawa 'yan gudun hijira shawara yadda zasu kare kansu

Gwamna Ortom ya bawa 'yan gudun hijira shawara yadda zasu kare kansu

- Gwamna Ortom na shawarci 'yan gudun hijira su koma gidajensu su kare kansu da duwatsu

- Gwamnan yace suyi koyi da Annabi Dawud a cikin Bible inda yayi amfani da dutse wajen kashe makiyinsa

- Ortom yace gwamnatin jihar bata da isashen kudaden da zata bude wata sabuwar sansanin 'yan gudun hijira

A ranar Talata, Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya shawarci al'ummar dake zaune a sansanin yan gudun hijira su koma gidajensu suyi amfani da duwatsu wajen kare kansu daga harin makiyaya.

Gwamnan ya fadi hakan ne yayin da ya bayyana cewa gwamnatinsa baza ta iya kulawa da yan gudun hijirar ba saboda haka su koma gidajen su.

Gwamna Ortom ya bawa 'yan gudun hijira shawara yadda zasu kare kansu

Gwamna Ortom ya bawa 'yan gudun hijira shawara yadda zasu kare kansu

Ortom yayi karin bayani inda yace kashekashen da akeyi a jihar yayi yawa har ta kai matsayin da al'umma ke gudu daga gidajen su.

DUBA WANNAN: Mai dakina na tura hotunan tsiraicinta ga kartin banza

Gwamnan ya bayar da wannan shawararce lokacin daya ziyarci sansanin yan gudun hijira da suka baro gidajensu bayan makiyaya sun kai musu hari a garuruwan Naka, dake karamar hukumar Gwer ta Yamma na jihar ta Binuwai.

Ortom yace kashe-kashen ya kazanta saboda haka ya shawarci al'ummar su kare kansu.

"A cikin Bible, Annabi Dawud yayi amfani da dutse wajen cin galaban kan makiyinsa, yanzu lokaci yayi da zaku koma gidajen ku, kuyi amfani da duwatsu don kare kanku a maimakon guduwa.

Gwamnan kuma yace gwamnatinsa tana aiki tare da masu sarautun gargajiya don ganin cewa an karfafa yan banga don su sami amincewar doka yadda zasu rika taimakawa jami'an tsaro wajen magance bata gari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel