Nigerian news All categories All tags
Mai dokar bacci ya ɓuge da gyangyaɗi: An kama jami’an Yansandan SARS guda 5 da laifin fashi da makami

Mai dokar bacci ya ɓuge da gyangyaɗi: An kama jami’an Yansandan SARS guda 5 da laifin fashi da makami

Rundunar Yansandan jihar Legas ta sanar da kama wasu jami’anta guda biyar a sakamakon kokarin yiwa wani mutumi mai suna Immanuel James fashi da makami, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yansandan sun hada da Sufetoci guda biyu, sai Sajan guda uku, dukkaninsu jamia’n rundunar yaki da yan fashi da makami, SARS, kuma sun yi kokarin yi ma James fashi ne a kan hanyar Ago-Palace, dake unguwar Okota na jihar Legas.

KU KARANTA: Yan Najeriya sun gudanar da zanga zangar nuna adawa da Tazarcen Buhari

Kaakakin runduar, SP Chike Oti ne ya tabbatar da kama baragurbin Yansandan a ranar Talata 10 ga watan Afrilu, sai dai ya musanta rahoton dake cewa jami’an rundunar SARS ne, haka zalika yace tuni an wanke Sufeta Jude Akhoyemta, bayan gaza samunsa da laifi da aka yi.

Mai dokar bacci ya ɓuge da gyangyaɗi: An kama jami’an Yansandan SARS guda 5 da laifin fashi da makami

Yansandan Najeriya

“Kamar yadda Kwamishinan Yansandan jihar Legas ya umarta, rundunar Yansandan jihar na shaida ma jama’a cewa mun gudanar da binciken kwakwaf game da rahoton da muka samu na kokarin yi ma Immanuel James fashi da makami,tare da cin zarafinsa, da ake zargin jami’an SARS sun yi.

“Mun gano jami’an da suka tafka wannan laifi, a yanzu haka ana cigaba da yi musu tambayoyi, kuma nan bada dadewa ba za’a gurfanar da su gaban kwamitin cikin gida don yake musu hukunci.” Ini shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel