Nigerian news All categories All tags
Sanatan Kaduna yana neman daukowa Shugaban Jam’iyyar APC Oyegun aiki

Sanatan Kaduna yana neman daukowa Shugaban Jam’iyyar APC Oyegun aiki

- Sanatan APC Shehu Sani yace a binciki Shugaban Jam’iyyar John Oyegun

- Shehu Sani ya kuma yabawa wasu ‘Yan Jam’iyyar APC irin su Bola Tinubu

- Tinubu sun tsaya tsayin-daka na ganin an yi sabon zaben Shugabanni a APC

Rikicin cikin gidan da ake fama da shi a Jam’iyyar APC mai mulki yana nema yayi kamari. Yanzu haka dai ku na da labari cewa Shugaban kasa Buhari da wasu sun nemi ka da su John Odigie-Oyegun su cigaba da zama a kujerun su.

Sanatan Kaduna yana neman daukowa Shugaban Jam’iyyar APC Oyegun aiki

Sanata Shehu Sani na Kaduna yace a binciki zargin da ke kan Oyegun

Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya yabawa wannan mataki da Shugaba Buhari da irin su Bola Tinubu su ka dauka. Sanatan yace ya kamata kuma a binciki irin badakalar da John Oyegun da Majalisar sa su ka tafka a ofis.

KU KARANTA: APC: Tsofaffin Gwamnoni da Ministoci sun faro dakon kujerar Oyegun

‘Dan Majalisar ya bayyana wannan ne a shafin sa na sada zumunta inda yace akwai bukatar a binciki zargin da ke wuyan Shugaban Jam’iyyar John Oyegun domin tsare APC da mutunci. Sanatan na APC yayi kira cewa a gudanar da zabe.

Kwamared Shehu Sani dai ya saba magana ne a kaikaice cikin salo ta shafukan sa na Facebook da Twitter. Shehu Sani ya jinjinawa ‘Yan Majalisa da Shugaban kasa da irin su Tinubu kan matakin da su ka dauka a Jam’iyyar mai mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel