Nigerian news All categories All tags
Jerin mutanen da ke shirin gaje kujerar John Oyegun a Jam’iyyar APC

Jerin mutanen da ke shirin gaje kujerar John Oyegun a Jam’iyyar APC

Yanzu haka dai kafar Shugaban Jam’iyyar APC na kasa John Odigie-Oyegun daya tayi waje inda ake tunanin yin zabe a Jam’iyyar. Mun kawo maku jerin mutanen da ke shirin gaje kujerar Shugaban Jam’iyyar mai mulki.

Jerin mutanen da ke shirin gaje kujerar John Oyegun a Jam’iyyar APC

Tsohon Sanata Ken Nnamani na neman babban kujerar Jam’iyyar APC

Daga cikin masu neman kujerar John Oyegun a APC akwai:

1. Adams Oshiomole

Wasu na ganin cewa tsohon Gwamnan Jihar Edo Adams Oshiomole ne zai dare kujerar ganin cewa yana tare da Bola Tinubu tun a Jam’iyyar ACN kuma na hannun daman Shugaban kasa Buhari ne.

2. Ken Nnamani

Ana tunanin cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ken Nnamani wanda babban Jigo ne a APC a Kudancin Najeriya yana cikin masu neman kujerar kuma yana iya dacewa.

KU KARANTA: Rigimar mu da Buhari ba za ta kare ba - Bukola Saraki

3. Don Etibet

Tsohon Ministan man fetur kuma tsohon Gwamnan kasar yana cikin wadanda ake tunani su ka sa ran su a kujerar na Shugaban Jam’iyyar na kasa idan har aka tashi zabe. Etibet ya taba rike ANPP.

4. Ogbonna Onu

Onu wanda Minista ne a Gwamnatin Buhari kuma tsohon Gwamnan Jihar Abia wanda da su aka yi adawa a Jam’iyyar ANPP yana sha’awar zama Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki

5. Clement Ebir

Akwai kuma Sanata Ebri wanda yayi Gwamnan Jihar Kuros-Ribas yana saurayi cikin masu neman kujerar Shugaban APC na kasa. Ebri yayi takara a Jam’iyyar ANPP kafin ya koma PPA a lokacin PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel