Nigerian news All categories All tags
Zaben 2019: An kara samun wanda ya fito takarar shugaban kasar Najeriya

Zaben 2019: An kara samun wanda ya fito takarar shugaban kasar Najeriya

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya watau Central Bank of Nigeria, CBN, mai suna Kingsley Moghalu da yanzu haka yake yaki neman zama shugaban kasar Najeriya ya bayyana cewa sai ya fi Buhari tabukawa idan har aka zabe shi.

Mista Kingsley Moghalu ya yi wannan ikirarin ne a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar ya kuma rabawa dauke da sa hannun sa biyo bayan bayyana kudurin sake tsayawa takara da shugaba Muhammadu Buhari yayi.

Zaben 2019: An kara samun wanda ya fito takarar shugaban kasar Najeriya

Zaben 2019: An kara samun wanda ya fito takarar shugaban kasar Najeriya

KU KARANTA: Sifeto Janar na yan sandan Najeriya ya sha kasa a kotu

Legit.ng ta samu cewa ya bayyana cewa shi idan aka zabe shi zai tabbatar da yawaitar arziki da kuma korar yunwa daga kasar sabanin halin da ake ciki na kunci yanzu sakamakon salon mulkin shugaban kasar.

A wani labarin kuma, Shugabannin jam'iyyar APC shiyyar kudu maso gabashin Najeriya a ranar Litinin din da ta gabata sun bayyana cewa tazarce nan da shugaba Muhammadu Buhari zai nema sune za su fi kowa cin gajiyar ta.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban jam'iyyar na shiyyar Cif Emma Eneukwu ta re da jami'in yada labaran jam'iyyar a shiyya Mista Hyacinth Ngwu suka sanyawa hannu a garin Enugu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel