Nigerian news All categories All tags
Babbar magana: Yan Najeriya suna gudanar da zanga-zangar kin-jinin tazarcen Buhari a Landan

Babbar magana: Yan Najeriya suna gudanar da zanga-zangar kin-jinin tazarcen Buhari a Landan

Fadar shugaban kasar Najeriya ta tabbatar da labarin cewa wasu 'yan Najeriya mazauna kasar Birtaniya sun soma yi wa shugaba Muhammadu Buhari zanga-zanga suna bukatar ya janye kudurin sa na sake tsayawa takarar da ya ayyana a zaben 2019 mai zuwa.

Sai dai daya daga cikin hadiman na shugaban kasa ya bayyana cewa wannan ba abunda yake nunawa sai tabbacin cewa shugaban kasar na kokarin dora kasar bisa turbar da ta dace ne shiyasa hakan ke ta faruwa.

Babbar magana: Yan Najeriya suna gudanar da zanga-zangar kin-jinin tazarcen Buhari a Landan

Babbar magana: Yan Najeriya suna gudanar da zanga-zangar kin-jinin tazarcen Buhari a Landan

KU KARANTA: Abu 8 da ka iya ba Buhari nasara a 2019

Legit.ng ta samu cewa wannan hadimin na shugaban kasa ya kara da cewa haka zalika duba da yadda gwamnatin shugaba Buhari din ke ta kokarin yaki da cin hanci da rashawa, hakan ya sanya dole wasu jiga-jigan barayin gwamnati suka shiga tashin hankali.

A wani labarin kuma, Babban minista a ma'aikatar sufuri na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Mista Rotimi Amaechi ya ayyana cewa shi da sauran ministocin Buhari suna karbar Naira dubu 950 ne kacal duk wata a matsayin albashi.

Mista Amaechi yayi wannan ikirarin ne a yayin da yake jawabin sa a wajen wani taron kaddamar da littafin da wani tsohon jami'in gwamnatin tarayya daga jihar ta sa marigayi Dakta Matthew Mbu, tsohon ministan harkokin wajen Najeriya ya wallafa mai taken 'Diginity In Service'.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel