Nigerian news All categories All tags
Yan Najeriya sun gudanar da zanga zangar nuna adawa da Tazarcen Buhari (Bidiyo)

Yan Najeriya sun gudanar da zanga zangar nuna adawa da Tazarcen Buhari (Bidiyo)

Wasu yan Najeriya mazauna birnin Landan sun shirya tare da gudanar da zanga zangar nuna adawa da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, da kuma nuna adawa da burinsa na tazarce da ya bayyana.

Legit.ng ta ruwaito yan Najeriyan sun gudanar da wannan zanga zanga ne da safiyar ranar Talata 10 ga watan Afrilu a gaban ofishin jakadancin Najeriya, inda suke dauke da sakonnin da suka hada da ‘Buhari ka kada ka tsaya takara’ da sauransu.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Kadun ta kama yan ‘Sara Suka’ 70 dake fitinan jama’an Kaduna

Sai dai fadar shugaban kasa ta tabbatar da zanga zangar, amma ta bayyana cewar yana adawar shugaban kasa Muhammadu Buhari, wadanda gwamnatinsa ta kama da laifin satar kudin al’umma ne suka dauki nauyin wannan zanga zanga, ta hanyar biyan masu zanga zangar.

Ga bidiyon zanga zangar kamar yadda Sholyment Olusegun Olusola ya daura a shafinsa na Facebook.

Majiyar daga fadar shugaban kasa ya bayyana cewar sun samo rahoto daga hukumomin tsaron sirri cewa wasu yan Najeriya zasu cigaba da gudanar da zanga zangar da nufin kunyata Buhari da gwamnatin Najeriya, sai dai yace babu abinda zai karkatar ma Buhari hankali game da abinda ya sa a gaba.

Yan Najeriya sun gudanar da zanga zangar nuna adawa da Tazarcen Buhari (Bidiyo)

Zanga zanga

“Sanarwa da Buhari yayi na neman Tazarce ne ya razana su, don haka suke biyan yan uwansu mazauna Landan da nufin su bata ma Buhari suna tare da gwamnatinsa, amma su sanu babu abinda zai fasa.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel