Nigerian news All categories All tags
Abubuwa 8 da ka iya baiwa shugaba Buhari nasara a 2019

Abubuwa 8 da ka iya baiwa shugaba Buhari nasara a 2019

Yayinda shugaban kasa ya alanta niyyar sake takararsa a zaben badi kuma domin bada daman muhawara da ilimantar da al’umma, jaridar Legit.ng ta kawo muku abubuwa bakwai da ka iya baiwa shugaba Muhammadu Buhari nasara a zaben 2019.

1. Yakin Boko Haram

Daga shekarar 2015 zuwa yanzu, rundunar sojin Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari sun samu manyan nasarori a kan yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram musamman a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Masu lura da lissafi sun bayyana cewa sabanin gwamnatocin da suka shude inda ake kai hare-haren Bam sassan Najeriya irinsu jihar Kano da Abuja, ba’a kai harin Bam ko daya wani jiha wajen yankin Arewa maso gabas ba.

Kana shugaba Buhari ya samu nasarar dawo da yan matan Chibok akalla 80 kamar yadda yayi alkawari kafin zaben 2018.

Gwamnatin Buhari ta samu nasarar fitittikin yan Boko Haram daga dajin Sambisa.

Abububa 8 da ka iya baiwa shugaba Buhari nasara a 2019

Abububa 8 da ka iya baiwa shugaba Buhari nasara a 2019

2. Yakin cin hanci da rashawa

Daga hawa karagar mulki, shugaba Muhammadu Buhari ya dumfari yakin cin hanci da rashawa. Matakin farko da ya dauka shine sauya nada wani kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da rashawa karkashin jagorancin Farfesa Itse Sagay, sannan ya nada shugaban hukumar EFCC Mista Ibrahim Magu.

Shugaban Buhari ya fara da amfani da asusun bai daya wato TSA domin toshe hanyoyin satan kudin gwamnati, ya damke Kanal Sambo Dasuki, kan laifin sama da fadi da kudin makamai, sannan aka kwato makudan kudi daga hannun barayi.

Hukumar EFCC ta gano kudade N521,815,000, $53,272,747, £122,890, da €547,730.

Abububa 8 da ka iya baiwa shugaba Buhari nasara a 2019

Abububa 8 da ka iya baiwa shugaba Buhari nasara a 2019

3. Asusun ajiyan kasashen waje wato (External reserves)

Asusun ajiyan kasashen waje wato External reserves ya karu daga kasa da $10 billion zuwa $46 billion cikin shekara 3.

4. Shirin N-power

Gwamnatin shugaba Buhari ta samar da aikin yi ga akalla matasa 200,000 inda ake biyansu N30,000 a wata. Wannan abu ya farantawa yan Najeriya rai saboda ya rage talauci da rashin aikinyi tsakanin matasa.

Abububa 8 da ka iya baiwa shugaba Buhari nasara a 2019

Abububa 8 da ka iya baiwa shugaba Buhari nasara a 2019

5.Ginin layin dogo na jiragen kasa

Gwamnatin shugaba Buhari ta harzuka ta karasa ayyukan layin dogo na jiragen kasa domin saukin sufurin yan Najeriya. Zuwa yanzu an kamala layin dogon Kaduna zuwa Abuja. Ana kan yin na Legas zuwa Kano, Lagos zuwa Fatakwal, Lagos zuwa Calabar. Wannan hanyoyin zai rasa dukkan jihohin Najeriya isan an kamala.

Abububa 8 da ka iya baiwa shugaba Buhari nasara a 2019

Abububa 8 da ka iya baiwa shugaba Buhari nasara a 2019

6. Gaskiya da amana

Har ila yau, yan Najeriya basu gushe suna ganin shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mutum mafi amana da gaskiya a fadin Najeriya.

7. Farin Jini

Har yanzu, ba’a samu dan Najeriyan da yafi Muhammadu Buhari farin jinni ba. Yadda al’ummar jihohi suka tarbesa a ziyarce-ziyarcen da ya kai kwanakin nan shaida ne ga haka.

Abububa 8 da ka iya baiwa shugaba Buhari nasara a 2019

Abububa 8 da ka iya baiwa shugaba Buhari nasara a 2019

8. Inganta wutan lantarki

A zamanin shugaba Buhari, karfin wutan lantarkin Najeriya ya kai 7,000 megawatts daga kasa da 4000 megawatts a shekarun baya.

Abububa 8 da ka iya baiwa shugaba Buhari nasara a 2019

Abububa 8 da ka iya baiwa shugaba Buhari nasara a 2019

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel