Nigerian news All categories All tags
An saki baturen da aka kama da giya a Saudiyya

An saki baturen da aka kama da giya a Saudiyya

Baturen kasar Ingila, Karl Andre; mai shekaru 74 ya samu 'yancinsa bayan hukumomi a kasar Saudiyya sun garkame shi saboda ya shiga da giya kasar.

An garkame Andre ne a kurkuku a Riyadh, babban birnin Saudi bayan samun sa da giya irin wacce ake iya hadawa a gida.

Saidai hukumomin kasar Saudiyya, a yanzu haka, sun saki mista Andre bayan shafe shekara guda a gidan yari.

Da yake bayyana halin da ya tsinci kansa bayan samun sa da giyar, Andre, ya bayyana cewar ya matukar jin kunya da kuma nadamar abinda ya aikata tare da bayyana shekara daya da ya shafe a gidan yari a matsayin wani darasi da ba zai manta da shi ba.

An saki baturen da aka kama da giya a Saudiyya

Carl Andre

Andre ya mika godiyar sa ga Firaministan kasar Ingila da kuma kuma sakataren ofishin jakadancin kasar Ingila a saudiyya, Philip Hammond, bisa rawar da suka taka wajen ganin ya samu 'yancinsa daga daurin da hukumomi suka yi masa a kasar ta saudiyya.

DUBA WANNAN: Dalibin jami'ar ATBU Bauchi ya mutu a ruwan wanka dake Yankari

Kazalika, ya mika godiyar sa ga iyalinsa bisa goyon baya da fahimtar da suka nuna yayin da ya tsinci kansa cikin mawuyacin halin da ya fada tare da bayyana cewar zai gina sabuwar rayuwa tare da iyalinsa.

Laifi ne babba a kasar Saudiyya a sha ko siyar da duk wani abun sha mai dauke da sinadarin giya.

Bin dokokin addinin Islama shine babban kalubale da bakin kasashen ketare da ba musulmi ba ke fuskanta a kasar Saudiyya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel