Nigerian news All categories All tags
Jerin Kasashe duniya da ba bu hukunci ga wadanda suka aikata Fyade

Jerin Kasashe duniya da ba bu hukunci ga wadanda suka aikata Fyade

A yayin da lamarin dabi'u a duniya ke ci gaba da tabarbarewa da sunan zamani, akwai wasu kasashe da ba su dauki fyade a bakin komai ba, inda masu wannan kazanta ke sha matukar sun amince za su auri wadanda suka ketawa haddi.

A wani bincike da sanadin shafin South China Morning Post ya bayyana cewa, akwai kasashe 73 a duniya da masu fyade ka iya shallake hukunci matukar sun amince za su auri wadanda suka ketawa haddi, irin su kasar Bahrain, Iraq, Philippines, Tajiskistan da kuma Tunisa.

Binciken ya kuma bayyana cewa, akwai jerin kasashe 10 da dokokin su sun amince da fyade matan aure da suka hadar har da kasar Ghana, Lesotho, Oman, Singapore da Sri Lanka.

A wasu ƙasashen, akan iya hukunta matar auren da ta yi korafin fyade muddin ta gaza bayar da shaidu da za su tabbatar an ci zarafin ta.

KARANTA KUMA: Ministan Noma ya bayyana dalilin da ka iya harzuka rikicin Makiyaya da Manoma a Najeriya

A wani binciken kuma da jaridar Legit.ng ta gudanar da sanadin shafin www.theclever.com ya bayyana cewa, akwai jerin kasashe 15 da ba su dauki cin zarafi da keta haddin mata a bakin komai ba, domin kuwa babu wani da dokar kasashen ta tanadar ga ma su aikata wannan laifi.

Kasashen sun hadar da; Burkina Faso, Haiti, Lebanon, Congo, Armenia, Ivory Coast, Egypt, Cameroon, Yemen, Latvia, Lesotho, Uzbekistan, Iran, Pakistan da kuma Nijar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel