Nigerian news All categories All tags
Wani mutumi ya haura kasashen Duniya 17 domin ya je aikin Umrah

Wani mutumi ya haura kasashen Duniya 17 domin ya je aikin Umrah

- Isaac Bannor ya zagaya kasashe sama da 10 wajen zuwa Umrah

- Wannan Bawan Allah ya zaga ne ba tare da hawa jirgin sama ba

- Bannor yace bai taba aikin Umrah ba don haka yace zai jarraba

Kowa dai da kiwon da ya karbe sa inji Hausawa don kuwa mun samu labarin wani Bawan Allah ‘dan asalin kasar Aljeriya mai suna Isaac Bannor da yayi tattaki na wata-da-watanni zuwa Kasa mai tsarki.

Wannan mutumi ya zagaya kasashe da yawa sai dai bai leka kasar Saudiyya ba don haka yace ya kamata ya zo yayi aikin Umrah. Wannan mutumi mai suna Bannor ya taka ne zuwa Saudi ba tare da jirgi ba ko mota ko babur.

KU KARANTA:

Bannor ya leka Kasashe 17 wanda su ka hada da Austria, Sloveniya, Kuroshia, Bosniya, Sabiya, Iran, Iraki, Kuwait, Bulgariya, Turkiyya, Jamus inda yace ya sha matukar wahala wajen tsallake Kasar Faransa da kuma kasar Austriya.

Isaac Bannor yayi wata 6 daga Kasar Faransa zuwa Kasar Saudi Arabia inda a kowace rana yake shafe kilomita 50. Bannor ya rika yawo ne da kayan shi a ‘yar amalanke.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel