Nigerian news All categories All tags
Boko Haram: Gobara ta tafka barna a sansanin yan gudun Hijira, mutane 14 sun kone

Boko Haram: Gobara ta tafka barna a sansanin yan gudun Hijira, mutane 14 sun kone

Akalla mutane goma sha hudu ne suka jikkata sakamakon kuna da suka samu daga wata gobara da ta tashi a sansanin yan gudun hijira dake garin Rann na jihar Borno, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan gobara ya faru bayan kimanin sati biyu da faruwar wata gobarar a sansanin, wanda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar. Sai dai a wannan gobarar da aka yi, babu wanda ya rasu, sai dai an samu mutane 14 da suka samu rauni, tare da kona dakuna fiye da dubu daya.

KU KARANTA: Jami’an Yansanda sun yi ram da yan kungiyar asiri, yan fashi da makami da barayin mutane 28

Wani jami’in Sojojin sa kai na Sibiliyan JTF ya tabbatar da faruwar gobarar, inda yace ta faru ne a sakamakon girke girke da yan gudun hijira ke yi, inda daga nan iska ke wartwatsa rushin wuta, a sanadiyyar haka sai gobara ta tashi.

Boko Haram: Gobara ta tafka barna a sansanin yan gudun Hijira, mutane 14 sun kone

Gobara a Rann

Jami’in mai suna Kaka Ari yace: “A cikin kwanaki uku mun samu gobara da dama a sassan sansanin yan gudun hijiran, wanda ya kona sama da dakuna dubu daya.”

Shi dai wannan sansani dake dauke da yan gudun Hijira akalla dubu tamanin, 80,000 ya sha gamuwa da ibtila’I daban daban, tun daga harin yan kunar bakin wake na Boko Haram, zuwa Gobara, kai har ma zuwa harin kuskure da Sojoji ke kaiwa sansanin da bama bamai daga jirgin sama.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel