Nigerian news All categories All tags
Mun gaji da gafara Sa: Jami’an hukumar Kwatsam sun yi bore game da sabon Inifam da aka kirkiro musu

Mun gaji da gafara Sa: Jami’an hukumar Kwatsam sun yi bore game da sabon Inifam da aka kirkiro musu

Da dama daga cikin Jami’an hukumar Kwastam sun nuna bacin ransu game da wani sabon Inifam, wato kayan sawa na yin aiki, da hukumar ta kirkiro musu, inda suka ce ba shi bane matsalarsu a yanzu ba.

A satin daya gabata ne dai hukumar ta kaddamar da sabon Inifam, wanda tace jami’anta zasu dinga amfani da shi tare da tsofaffin inifam din, mai kalar riga fari, wanda kuma ruwan toka.

KU KARANTA: Ranar kin dillanci: Jami’an Yansanda sun yi ram da yan kungiyar asiri, yan fashi da makami da barayin mutane 28

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin hukumar, Joseph Attah yana cewa wannan na daga cikin gyaran fuska da garambawul da shugaban hukumar, Hamid Ali ke yi don kara ma aikin kima, martaba da daraja.

Mun gaji da gafara Sa: Jami’an hukumar Kwatsam sun yi bore game da sabon Inifam da aka kirkiro kusu

Sabon Inifam

Sai dai wasu manyan hafsoshin hukumar sun soki wannan mataki, inda suka ce hakan ba zai yi wani tasiri a aikinsu ba. Samuel Affikku ya bayyana a shafinsa a Facebook cewa: “Karin albashi da alawus alawus muke nema, mun gaji da gafara sa, bamu ga kaho ba.”

Wani cewa yayi: “Ina ma za’a baiwa jami’an hukumar kudin inifam din ne, hakan ne kadai zai kara musu kwarin gwiwar gudanar da aikinsu yadda ya kamata, a zamanin nan, mutane na neman hanyar samun kudi ne banda albashi.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel