Nigerian news All categories All tags
Ana barazanar kasheni dan ba zan goyi bayan Wike ba a 2019 ba – Shugaban Hausawan kudu

Ana barazanar kasheni dan ba zan goyi bayan Wike ba a 2019 ba – Shugaban Hausawan kudu

Shugaban Hausawan Kudu maso Kudu da Kudu maso yammacin Najeriya, Alhaji Musa Saidu, yace babban hadimin gwamnan jihar RIbas, Nyesom Wike, ya yi barazanar kasheshi don bai goyon bayan Wike a 2019.

Alhaji Musa Saidu, ya rubuta wasika ga sifeton yan sanda, dirakta janar na DSS, fadar shugaban kasa, ta hannun lauyansa, Eze Kpaniku, cewa wannan babban jami’in gwamnatin Wike ya gayyacesa wata ganawa tare da Alhaji Jabi Mohammed a ofishinsa.

Ya ce kafin sun kara ofishin, kwamishanan ya tara wasu yan bindiga tare da shi suka rutsasu a cikin gareji.

Ana barazanar kasheni idan ban goyi bayan Wike ba a 2019 – Shugaban Hausawan kudu

Ana barazanar kasheni idan ban goyi bayan Wike ba a 2019 – Shugaban Hausawan kudu

A cewarsa: “ Ya fito da wani jarida inda ya tamyemi me yasa yace kada mutane su zabi gwamnan? Sai nace ni ban fadi hakan ba,”.

KU KARANTA: Ku manta da maganar da Buhari yayi a 2011 na cewa sau daya zai yi mulki - Femi Adesina

Saidu yace kwamishanan ya umurci dan sanda ya kasheshi amma da ikon Allah, dan sandan ya ki.

Daga baya dan sanda ya raka har cikin motarsa ya samu ya gudu daga wajen.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel