Nigerian news All categories All tags
Ranar kin dillanci: Jami’an Yansanda sun yi ram da yan kungiyar asiri, yan fashi da makami da barayin mutane 28

Ranar kin dillanci: Jami’an Yansanda sun yi ram da yan kungiyar asiri, yan fashi da makami da barayin mutane 28

Rundunar Yansandan jihar Edo ta sanar da cafke wasu miyagun mutane guda 28 a garin Bini wadanda suka fitini Jihar, da suka kunshi yan kungiyar matsafa, yan kungiyar asiri, yan fashi da makami da kuma masu garkuwa da mutane.

Kwamishinan Yansandan jihar, Johnson Kokumo ne ya sanar da haka a ranar Talata 10 ga watan Afrilu yayin da yake ganawa da manema labaru, inda yace rundunar ta samu nasarorin nan ne a cikin sati biyun da suka gabata.

KU KARANTA: Yadda Maza suka mayar da sakin Mata kamar ruwan sha na bani tsoro – Inji Sarkin Kano

Legit.ng ta ruwaito Kwamishina Kokuma yana fadin cewa guda hudu daga cikinsu gagararrun masu garkuwa da mutane ne, 11 kuma sun yi kaurin suna wajen fashi da makami, yayinda sauran 13 kuma suka ciri tuta a harkar tsafe tsafe da bin kungiyoyin asiri.

Ranar kin dillanci: Jami’an Yansanda sun yi ram da yan kungiyar asiri, yan fashi da makami da barayin mutane 28

Miyagu

Dansandan ya cigaba da cewa sun kwato makamai da suka hada da bindigar AK 47, Alburusai, bindigar toka, adda, wuka, da wasu kayan tsubbace tsubb daga hannun barayin mutanen.

Yayin da yansandan suka yi nasarar kwato bindigogi guda biyu, alburusai, wayoyi guda ashirin da uku, guduma, kudi naira dubu goma sha tara da motoci guda biyu kirar Marsandi da kirar Volkswagen daga wajen yan fashin.

Sai kuma yan kungiyar matsafan da suka mika ma Yansanda bindigu guda biyu, alburusai, da wayoyi guda uku. Daga karshe Kwamishinan ya bada tabbacin zasu cigaba da jajircewa wajen yaki da miyagun ayyuka a jihar, sa’anann ya yaba da kokarin sauran hukumomin tsaro dake jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel