Rabon kwaɗo baya hawa sama: Buhari ya naɗa wasu mutane 26 muhimman mukamai

Rabon kwaɗo baya hawa sama: Buhari ya naɗa wasu mutane 26 muhimman mukamai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika ma majalisar dattawa sunan wani fitaccen lauya dake zama a jihar Kaduna, Festus Okoye da nufin tantance shi don ya nada shi mukamin kwamishina a hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC.

Premium Times ta ruwaito shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ne ya karanta wasikar shugaban kasa a zaman majalisa na ranar Talata, 10 ga watan Afrilu, inda a ciki Buhari ya bayyana ya yi nufin nada Festus ne don ya zamo wakilin yankin Kudu maso gabashin kasar nan a hukumar INEC.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta maka yaron wani tsohon gwamna Kotu bisa karkatar da kudi naira biliyan 1.5

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Festus Okoye dan asalin jihar Imo ne, kuma shugaban kungiyar kare hakkin bil adama, Human Right Monitor. Haka zalika Buhari ya bukaci majalisar ta tantance mutane biyu, Abb Ali daga Katsina da Mohammed Sagir daga Neja a matsayin hukumar kula da ma’aikatan shari’a ta kasa.

Bugu da kari, Buhari ya bukaci majalisar ta tantance mutane 23 don nada su kwamishinonin hukumar kidaya ta kasa, ya aika sunayensu nasu kamar haka: Nwanne Johnny Nwabuisi (Abia), Dr Clifford Zirra (Adamawa), Chidi Christopher Ezeoke(Anambra), Barrister Isa Audu Buratai (Borno), Charles Iyam Ogwa(Cross River), Richard Odibo(Delta), Okereke Darlington Onaubuchi (Ebonyi) da A.D. Olusegun Aiyajina (Edo).

Sauran sun hada da Ejike Ezeh (Enugu), Hon. Abubakar Mohammed Danburam (Gombe), Uba S.F. Nnabue (Imo), Abdulmalik Mohammed Durunguwa (Kaduna), Sulaiman Ismaila Lawal (Kano), Jimoh Habibat Isah (Kogi), Sa’adu Ayinla Alanamu (Kwara), Nasir Isa kwarra (Nasarawa).

Daga karshe akwai Barrister Aliyu Datti (Niger), Yeye Seyi Adererinokun Olusanya (Ogun), Prince Oladiran Garvey Iyantan (Ondo), Senator Mudashiru Oyetunde Hussain (Osun), Cecilia Arsun Dapoet (Plateau), Ipalibo Macdonald Harry (Rivers), Sale S. Saany (Taraba).

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel