Nigerian news All categories All tags
Da duminsa: Buratai ya haramtawa jami'an soji bauta a Cocin wajen bariki

Da duminsa: Buratai ya haramtawa jami'an soji bauta a Cocin wajen bariki

- Shugaban sojin kasar na kasa, Lt.-Gen. Tukur Buratai, ya haramtawa duk wani sojan kasar nan zuwa majami'a dake wajen barikin soja don aiwatar da ibada

- Laftanal Janar Buratai ya bayar da wannan gargadin wajan wani taron soji da ya wakana jiya a Abuja

- Yace, daga yanzu, babu wani jami'in soja da muka yarjewa zuwa cocin da ba na bariki, duk da cewa akwai wadatattun majami'u da masallatai a cikin barikin

Shugaban sojin kasa na kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya haramtawa duk wani sojan kasar nan zuwa duk wata majami'a dake wajen barikin soja don aiwatar da ibada.

Da duminsa: Buratai ya haramtawa jami'an soji bauta a Cocin wajen bariki

Buratai

Janara Buratai ya bayar da wannan gargadi ne wajen wani taron soji da ya wakana jiya a Abuja. Buratai yace, duk wani jami'in soja da yake son shiga wani sha'ani, imma na siyasa, na addini ko kabilanci, yana mai bashi shawara da yayi ritaya ta kashin-kansa, in yaki kuwa, duk abinda ya biyo baya, to ya zargi kansa.

DUBA WANNAN: Sunan da na fi son ake kiran mahaifina da shi - Diyar shugaba Buhari, Zarah Indimi

Yace, "daga yanzu, babu wani jami'in soja da muka yarjewa zuwa cocin da ba a cikin bariki suke ba, tunda akwai wadatattun majami'u da masallatai a cikin barikin."

Bisa alamu dai, gargadin ba zai rasa nasaba da karatowar kakar zabe ta 2019 ba, inda ake ta samun shugabannin addinai na fadakar da jama'a da su je su yi rijistar zabe domin yin amfani da ita a kan wanda suke son a zaba, sakamakon matsalar tsaro da wasu ke ganin kiristoci na fama da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel