Nigerian news All categories All tags
Buhari 2019: Cigaba ne mai kyau - Shagari

Buhari 2019: Cigaba ne mai kyau - Shagari

- Aminu Shagari mamban majalissar wakilai (APC-Sokoto) yace kudirin Buhari na sake tsayawa takara a 2019 cigaba ne wanda jam’iyyar APC ta samu

- Shagari yace tinda ba wanda ya fito fili ya bayyana kudirin tsayawa takarar shugaban kasa daga jam’iyyar, abu ne mai kyau da Buhari ya bayyana nasa kudirin

- Shagari yace sake tsayawar Buhari takarar shugaban kasa yana da kyau saboda yanada manufa mai kyau akan Najeriya

Aminu Shagari mamban majalissar wakilai (APC-Sokoto), a ranar 9 ga watan Afirilu ya bayyanawa Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, a birnin tarayya, cewar kudirin Buhari na sake tsayawa takara a 2019 cigaba ne wanda jam’iyyar APC ta samu.

Shagari ya fadawa NAN, a ranar Litinin, cewa tinda ba wanda ya fito fili ya bayyana kudirin tsayawa takarar shugaban kasa daga jam’iyyar, abu ne mai kyau da Buhari ya bayyana nasa kudirin.

Shagari yace sake tsayawar Buhari takarar shugaban kasa yana da kyau saboda “yanada manufa mai kyau akan mutanen Najeriya.

Buhari 2019: Cigaba ne mai kyau - Shagari

Buhari 2019: Cigaba ne mai kyau - Shagari

"Ya kawo cigaba da dama ga tattalin arzikin Najeriya, don shi mai gaskiya ne,wanda shine babban abun dubawa,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: 2019: ‘Yan APC dake Ingila sun sha alwashin biyawa Buhari kudin fom na tsayawa takara

Dan Majalissar yace shugaba Buhari yana kokari sosai a fannin yaki da cin hanci na kawo karshensa a Najeriya.

Haka zalika Sanata Shehu Sani yace bayyanawar kudurin Buhari na tsayawa takarar shugaban kasa 2019, ya magance duk wani mai kudurin tsayawa takarar daga jam’iyyar APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel