Nigerian news All categories All tags
2019: ‘Yan APC dake Ingila sun sha alwashin biyawa Buhari kudin fom na tsayawa takara

2019: ‘Yan APC dake Ingila sun sha alwashin biyawa Buhari kudin fom na tsayawa takara

- ‘Yan Jam’iyyar APC dake kasar Ingila sunce zasu siyawa Buhari form na sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2019

- Jacob Ogunseye mai magana da yawun kungiyar, ya bayyana alkawalin da suka dauka a birinin tarayya bayan shugaba Buhari ya bayyana kudurinsa na sake tsayawa takara 2019

- Kungiyar tace ta gamsu da sake tsayawar shugaban kasar takara, kuma hakan zai karawa Najeriya karfi da kuma mutuncin siyasa a kasar

‘Yan Jam’iyyar APC dake kasar Ingila sunce zasu siyawa Buhari form na sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2019.

Jacob Ogunseye mai magana da yawun kungiyar, ya bayyana alkawalin da suka dauka a ranar Talata, a birinin tarayya, bayan shugaba Buhari ya bayyana kudurinsa na sake tsayawa takara 2019, a ranar Litinin.

2019: ‘Yan APC dake Ingila sun sha alwashin biyawa Buhari kudin fom na tsayawa takara

2019: ‘Yan APC dake Ingila sun sha alwashin biyawa Buhari kudin fom na tsayawa takara

Kungiyar tace ta gamsu da sake tsayawar shugaban kasar takara, kuma hakan zai karawa Najeriya karfi da kuma mutuncin siyasa a kasar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shema yaki amincewa da laifuka 24 da hukumar EFCC ke tuhumarsa akansu

Kungiyar ta kara da cewa sake zabar shugaba Buhari karo na biyu zai karawa tattalin arzikin kasar da siyasar Najeriya mutunci a idon duniya. Saboda haka suke kira ga ‘yan Najeriya dake ko ina a fadin duniya da su sake marawa Buhari baya, don taimakawa Najeriya ta daidaita.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel