Nigerian news All categories All tags
Mutuwar mambobi: Majalisar dattijai ta daga zamanta na yau, ta saka ranar dawowa

Mutuwar mambobi: Majalisar dattijai ta daga zamanta na yau, ta saka ranar dawowa

A yau ne majalisar dattijai ta daga zamanta domin nuna alhinin mutuwar mambobin majalisar guda biyu.

Dan majalisa, Marigayi Umar Jibril, mai wakiltar mazabar Lokoja/Kogi a majalisar wakilai, ya mutu ranar ranar 30 ga Maris, 2018.

Kafin mutuwar sa, shine mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai.

Kwanaki biyar bayan mutuwar sa, Allah ya yiwa Sanata mai wakiltar jihar Katsina ta Arewa, Bukar Mustapha, rasuwa bayan wata gajeriyar jinya.

Mutuwar mambobi: Majalisar dattijai ta daga zamanta na yau, ta saka ranar dawowa

Majalisar dattijai

Majalisar wakilai ta amince da daga zamanta bayan shugaban masu rinjaye a majalisar, Ahmed Lawan, ya gabatar da kudirin bukatar hakan.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga cikin kakin 'yan sanda sun kashe DPO

Mambobin majalisar sun yi tsit na tsawon minti guda domin nuna girmamawa ga mamatan.

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana cewar majalisar zata gudanar da zama na musamman a gobe, Laraba, ranar da majalisar zata dawo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel