Nigerian news All categories All tags
Dalilai 7 da za su sanya shugaba Buhari ya yi tazarce a zaben 2019

Dalilai 7 da za su sanya shugaba Buhari ya yi tazarce a zaben 2019

A yayin da yau kwana guda kenan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kudirin sa na sake tsayawa takara a zaben 2019, Legit.ng ta hikaito muku jerin wasu muhimman ababe 7 da za su sanya ya yi nasara a zaben.

Dalilai 7 da za su sanya shugaba Buhari ya yi tazarce a zaben 2019

Dalilai 7 da za su sanya shugaba Buhari ya yi tazarce a zaben 2019

Rahotanni da suke ta kai komo a fadin kasar nan sun bayyana cewa, a yayin da wasu ke murnar wannan kudiri na shugaban kasa, wasu ko sun bayyana ra'ayin cewa lallai zai sha kashi tamkar yadda tsohon shugaban kasa Goodluck ya kwashi na sa a hannu.

Ga jerin ababe bakwai da jaridar Legit.ng ta ke hasashen za su kara kaimi wajen nasarar shugaba Buhari a zaben 2019:

1. Yadda ake ci gaba da galaba akan ta'addancin Boko Haram

2. Yakar cin hanci da rashawa

3. Tumbastsar asusun Najeriya dake kasashen waje.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya bayyana dalilin sa na sake tsayawa takara

4. Samar da abin yi ta hanyar shirin N-Power ga matasa

5. Juyin juya hali a harkokin bunkasa noma

6. Karuwar samar da kudaden shiga a kasar nan

7. Dumbin masoya da shugaba Buhari yake da su a fadin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel