Nigerian news All categories All tags
Shugaba Buhari ya tsallake tarkona – Inji Ganduje

Shugaba Buhari ya tsallake tarkona – Inji Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya nuna jin dadi ga hukuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari na sake takara a zaben 2019.

Dailytrust ta rawaito cewa gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce shugaba Buhari ya tsallake tarkonsa a game da zaben 2019 bayan ya bayyana ra’ayinsa na sake tsayawa takarar shugabancin kasa a shekarar 2019.

A wata sanarwa daga kwamishinan bayanai, Malam Muhammad Garba, ya ba da tabbacin cewa tazarcen Buhari zai tabbatar da cigaban nasarorin da gwamnatinsa tayi wajen ci gaban tattalin arziki, tsaro da kuma yaki da rashawa dake gwamnati.

Shugaba Buhari ya tsallake tarkona – Inji Ganduje

Shugaba Buhari ya tsallake tarkona – Inji Ganduje

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya Buhari ya cancanci a kara zabarsa a shekarar 2019 - APC

Kwamishinan yace mutanen Kano da gwamna Ganduje zasu tabbatar da ganin cewa Buhari ya ni nasara a zabe mai zuwa.

A baya Legit.ng ta tattaro cewa APC sun bayyana dalilansu na cewa ‘yan Najeriya zasu sake zabar shugaba Buhari a zaben 2019.

Sun bayyana haka a ranar Litinin lokacin da suke zantawa da ma’aikatan gidan Talabijin na Channels. Sakatare jam’iyyar APC, Bolaji Abdullahi yace sake zaben Buhari a matsayin shugaban kasa ra’ayin ‘yan Najeriya ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel