Nigerian news All categories All tags
'Yan sanda sun damke wani dan fashi daya kware ta hanyar amfani da Keke Napep

'Yan sanda sun damke wani dan fashi daya kware ta hanyar amfani da Keke Napep

- Hukumar Yan sanda tayi ram da wani dan fashi da ya kware ta hanyar amfani da keke napep

- Dan fashin yana sanya kaya ne irin na jami'an tsaro kuma ya tare mutane a wurin da babu zirga-zirga sosai yayi musu fashi

- Bayan an cafke shi, ya amsa laifinsa inda yace sharrin shedan ne ya jefa cikin wannan barnar

Hukumar Yan sandan Najeriya reshen jihar Enugu ta damke wani mutum da ake zargi da aikata fashi da makami ta hanyar amfani da babur mai kafa uku wanda akafi sani da Keke Napep ko a daidaita sahu.

A sanarwar daya bayar, Kakakin rundunar Yan sandan Enugu, Sufritandant Ebere Amaraizu yace an cafke wanda ake zargin ne a kusa da kasuwar masu sana'o'in hannu da ke Enugu a ranar 8 ga watan Afrilu.

'Yan sanda sun damke wani dan fashi daya kware ta hanyar amfani da Keke Napep

'Yan sanda sun damke wani dan fashi daya kware ta hanyar amfani da Keke Napep

KU KARANTA: Kungiyar kwadago na kasa ta bukaci karin albashi mafi karanci a Najeriya

Amaraizu yace dakarun yaki da yan kungiyar asiri na rundunar Yan sandan ne suka gano wanda ake zargin, Chika Ezike bayan sun sami bayannan sirri bisa wasu ayyukan fashin dayake aikatawa kana ya tsere.

"A cewar Yan sandan, wanda ake zargin ya amsa laifinsa inda ya ce yana yin shiga ce irin ta jami'an tsaro lokacin da yake tuka babur din, idan ya samu mutane a wuraren da babu al'umma sosai, sai yayi musu fashi kana ya gudu zuwa wani unguwar daban.

"Wanda ake zargin yace yayi nadamar abin daya aikata inda yace sheda ne ya hurre masa kunne."

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kakakin na rundunar Yan sanda yace wanda ake zargin yana bayar da hadin kai wajen taimaka wa Yan sanda da binciken da suke cigaba da gudanarwa.

Amaraizu yayi kira ga al'ummar jihar suyi takatsantsan da masu nufin su da sharri tare da sauran bata gari da ke yawo a wurare daban-daban.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel