Nigerian news All categories All tags
Majalisar Kasar Somaliland ta zartar da dokar daukan fyade a matsayin laifi

Majalisar Kasar Somaliland ta zartar da dokar daukan fyade a matsayin laifi

Rahotanni da sanadin shafin jaridar PM News sun bayyana cewa, majalisar dokoki ta kasar Somaliland ta zartar da dokar hukuncin dauri na shekaru 20 a gidan wakafi ga duk wanda ya aikata laifin fyade domin kawo karshen cin zarafin mata.

Wannan doka da majalisar ta zartar kamar yadda wani babban jami'i na kasar ya bayyana, ta kuma zartar da laifin kan wasu nau'ikan cin zarafi da suka hadar da auren dole, fataucin mata domin jima'i da kuma keta mu su haddi.

Ayan Mahmoud, wanda shine jakadan Somaliland a kasar Birtaniya yake cewa, wannan doka ta nemi amincewar majalisar kasar tun shekaru aru-aru da suka gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin shugaban kasar Musa Abdi da aka zaba a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, ta sanya kawo karshen cin zarafin mata da keta mu su haddi a cikin manufofin da ta sanya a gaba.

KARANTA KUMA: Yadda Sukari ke warkar da kekasassun Raunuka

A halin yanzu wannan kasa mai dauke da al'umma kimanin miliyan hudu tun samun 'yancin kai da tayi daga kasar Somalia a shekarar 1999, tana sa ran shugaban kasar ta ya rattaba kan wannan sabuwar doka cikin makonni ma su gabatowa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel