Nigerian news All categories All tags
Dalilin da ya sanya Buhari ya cancanci a kara zabarsa a shekarar 2019 - APC

Dalilin da ya sanya Buhari ya cancanci a kara zabarsa a shekarar 2019 - APC

- APC sun bayyana dalilansu na cewa ‘yan Najeriya zasu sake zabar shugaba Buhari a zaben 2019

- Sakatare jam’iyyar APC, Bolaji Abdullahi yace sake zaben Buhari a matsayin shugaban kasa ra’ayin ‘yan Najeriya ne

- Shugaba Buhari ya fadawa shuwagabannin jam’iyya cewa dalilin sake tsayawarsa takara ya biyo bayan bukatar bukatar mutanen Najeriya akan cewa ya sake tsayawa takara a zaben 2019

APC sun bayyana dalilansu na cewa ‘yan Najeriya zasu sake zabar shugaba Buhari a zaben 2019. Sun bayyana haka a ranar Litinin lokacin da suke zantawa da ma’aikatan gidan Talabijin na Channels.

Sakatare jam’iyyar APC, Bolaji Abdullahi yace sake zaben Buhari a matsayin shugaban kasa ra’ayin ‘yan Najeriya ne.

“Ina ganin cewa ‘yan adawa sunada masaniyyar cewa shekaru hudu basu isar gwamnati ta cimma gurinta na ayyukan da takeso ta gudanar, amma dai yin hakan zai taimakawa ayyukan da aka fara su cigaba”, inji shi.

Shugaba Buhari ya fadawa shuwagabannin jam’iyya a taron sirri da suka gudanar a birnin tarayya, cewa dalilin sake tsayawarsa takara ya biyo bayan bukatar bukatar mutanen Najeriya akan cewa ya sake tsayawa takara a zaben 2019.

Dalilin da ya sanya Buhari ya cancanci a kara zabarsa a shekarar 2019 - APC

Dalilin da ya sanya Buhari ya cancanci a kara zabarsa a shekarar 2019 - APC

“Shugaba Buhari ya kawo wani abu a Najeriya na daban, abun kuma shine yaki da cin hanci wanda wani lokaci muna mancewa da muhimmancinsa ga kasar nan”, inji mai magana da yawun jam’iyyar APC.

KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Mata a jihar Bauchi sun samar da hanyar gargajiya ta sarrafawa da adana Tumatir

Yace maganganu da akeyi game da cin hanci a kowace rana a fadin Najeriya, ya nuna cewa mutanen Najeriya basu yadda da cin hanci ba a matsayin wata hanya ta rayuwa a kasar nan ba, hakan yasa mutane ke bukatar shugaba Buhari da ya sake tsayawa takara a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel