Nigerian news All categories All tags
2019: Za muyi nasara akan shugaba Buhari - PDP, Accord

2019: Za muyi nasara akan shugaba Buhari - PDP, Accord

Bayan kwana guda da bayyana kudirin shugaban kasa Muhammadu Buhari na sake tsayawa takara a zaben 2019, jam'iyyun Accord da kuma PDP rassan jihar Oyo, tuni sun bayyana hasashen su na yadda za su lallasa shi tare da jam'iyyar sa ta APC.

Sakatarorin jam'iyyun biyu sun bayyana cewa, sanarwar shugaba Buhari ta sake tsayawa takara ta kara haskaka dama ta samun nasarar jam'iyyun su a zaben 2019.

Mista Wasiu Emiola, sakataren jam'iyyar PDP na jihar ta Oyo ya bayyana cewa, bayyana ƙudirin shugaba Buhari na yin tazarce ya ƙara sauƙaƙa dama ta lallasa shi a zaben shugaban ƙasa na 2019.

Shi kuwa sakataren jam'iyyar Accord Mista John Igbinsola ya bayyana cewa, bayyana kudirin shugaba Buhari ya maishe shi tamkar dan wasan kwaikwayo a sakamakon bin son zuciyar wasu 'yan siyasa dake tunzura shi.

KARANTA KUMA: Buhari zai kama hanyar birnin Landan a ranar Litinin

Igbinsola ya yi ikirarin cewa, gwamnatin APC cike take da mulkin kama karya da son kai na kyautatawa 'yan uwa doriya da yaƙin ta na cin hanci da rashawa da yake ƙasa da tsammanin 'yan Najeriya.

A yayin haka kuma, wani lauya na birnin Ibadan Mista Emmanuel Ajayi, ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin kasa ya bayar da dama ga shugaban kasa ya sake neman takara a karo na biyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel