Nigerian news All categories All tags
kaka-kara-kara: Digirin wasu yan Najeriya ya kusa zama takardar tsire

kaka-kara-kara: Digirin wasu yan Najeriya ya kusa zama takardar tsire

- Gwamnatin Najeriya na shirin shigo da tsarin da zai hana amfani da digirin bogi

- in dai wannan tsari ya tabbata, to digirin mutane da yawa zai zama tamkar takardar tsire

Ministan ilimi na kasa, Malama Adamu Adamu ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta dakatar da yarda da takardun digiri daga wasu makarantu da suke bayarwa, musamman a kasashen jamhuriyar Benin da Togo da Ghana da kuma Cameroon.

Gyaran ilimi: Gwamnatin Najeriya ta soke digiri daga kasashe 4, za’a cigaba da tantance 40,000 na kasashen waje

Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu

Da yake jawabin a jiya Litinin, yayin kafa kwamiti mai mutane 16 da zai tantance digirin da yan Najeriya keyi da yawansu yakai 40, 000 a kasashen waje, Ministan ilimin Malam Adamu yace, wannan tantancewa ta biyo bayan yawaitar korafi daga bakin al’umma dangane da makarantun bogin da basu cika ka’idar zama cikakkun makarantun da ya kamata su bayar da digiri ba, kuma soke takardun ma’aikatun gwamnati kadai zai shafa ba, har ma da masana’antu masu zaman kansu.

A wani bincike da ma’aikatar ilimi tayi, sun gano kusan kimanin yan Najeriya 40,000 ne ke karatu ko suke rike da takardun digirin bogin a makarantu daban-daban dake nahiyarmu ta Africa.

KU KARANTA: Jami'an SARS sun kulle dan kasuwa a bandakin banki saboda ya ki yi masu alheri

A saboda haka, Ministan ya kafa kwamitin domin tantance dokoki da sharrudan da digirin kasar wajen zai cika, kafin a yarda da shi. Kuma yanzu gwamnati tayi tsarin da sai ta bincika gami da amincewa da makarantar da masu son suyi karatu a cikinsa

“Amincewar da gwamnati za tayi ga masu son zuwa kasar waje karatu, na da mutukar muhimmanci ga makomar yan Najeriyar da zasu mallaki takardar shaidar kammala karatu daga kasashen wajen.” Ministan ya shaida.

Kwamitin dai an kaddamar da shi ne a yayin taron tantance takardun karatun yan kasar waje na kasa karo na 33.

Daga cikin aiyukan da kwamitin zai nayi sun hada da, gindaya sharruda da dokokin da gwamnatin Najeriya ke bukata kafin amincewa da takardar shaidar digiri daga kasar waje.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel