Nigerian news All categories All tags
Ministan Noma ya bayyana dalilin da ka iya harzuka rikicin Makiyaya da Manoma a Najeriya

Ministan Noma ya bayyana dalilin da ka iya harzuka rikicin Makiyaya da Manoma a Najeriya

Ministan Noma na Najeriya Cif Audu Ogbeh, ya yi gargadi akan abin da ka iya hazuka rikici tsakanin makiyaya da manoma a shekarar 2019, inda ya ce muddin ba a dauki mataki na kirkirar yankunan kiwo ba to kuwa samun ingataccen tsaro na satar shanu ba zai ta tabbatu ba.

Cif Ogbeh ya yi wannan kira ne a yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan taron cibiyar tsaro da kulawar abinci da aka gudanar a babban birnin na tarayya.

Mambobin kwamitin wannan cibiya sun nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari akan gaggawar bayar da lamunin sa na kirkirar yankunan kiwo.

Ministan Noma; Cif Audu Ogbeh

Ministan Noma; Cif Audu Ogbeh

Kwamitin ya kuma nemi shugaba Buhari wajen samar da matakan horo na musamman ga wasu masana harkokin noma da za su taimakawa hukumomin tsaro shawo matsalar rikicin makiyaya da manoma da a yanzu daruruwan rayuka sun salwanta.

KARANTA KUMA: Wasu 'yan ta'adda sun kashe Matafiya 10 a jihar Benuwe

Legit.ng da sanadin jaridar Vanguard ta fahimci cewa, kasancewar shugaba Buhari jagoran wannan kwamiti, gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu shine ya jagoranci taron a sakamakon rashin shugaba Buhari da ya kama hanyar sa ta zuwa birnin Landan bayan ya halarci taron shugabannin jam'iyyar su ta APC.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa, a yayin halartar taron shugabannin jam'iyyar ne, shugaba Buhari ya bayyana kudirin sa na sake tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel