Nigerian news All categories All tags
Tazarce: Ya kamata ka barwa matasa mulkin Najeriya – Kungiyar matasan Arewa ga Buhari

Tazarce: Ya kamata ka barwa matasa mulkin Najeriya – Kungiyar matasan Arewa ga Buhari

- Matasan jihohi 19 na Arewa a karkashin kungiyar matasa ta NYF sunyi kira ga shugaba Buhari da ya sake tinani game da tsayawa takarar shugaban kasa a karo na biyu

- Kungiyar tace abu daya da Buhari yake dashi shine aminci, amma sunce aminci kadai bazai isa kai Najeriya zuwa matsayin da ya kamataba a wannan zamanin

- Shugaban kungiyar Bobai Mathew Victor, sun bayyana cewa suna aiki ne ga Sanata Ahmed Makarfi dan takarar shugaban kasa

Matasan jihohi 19 na Arewa a karkashin kungiyar matasa ta NYF sunyi kira ga shugaba Buhari da ya sake tinani game da tsayawa takarar shugaban kasa a karo na biyu, ya barwa matasa su jagoranci kasar zuwa cigaban da take bukata.

Kungiyar jiya a garin Kaduna tace abu guda wanda Buhari yake dashi shine aminci, amma sunce aminci kadai bai isa ya jagoranci Najeriya zuwa matsayin da ya kamataba a wannan zamanin.

Tazarce: Ya kamata ka barwa matasa mulkin Najeriya – Kungiyar matasan Arewa ga Buhari

Tazarce: Ya kamata ka barwa matasa mulkin Najeriya – Kungiyar matasan Arewa ga Buhari

Shugaban kungiyar Bobai Mathew Victor, lokacin da suka kai ziyara ga kungiyar manema labarai ta Najeriya, NUJ, kungiyar ta bayyana cewa suna aiki ne ga Sanata Ahmed Makarfi dan takarar shugaban kasa, saboda mun yadda cewa tinaninsa shine irin wanda muke bukata don cigaban kasar nan.

KU KARANTA KUMA: Sai Buhari yayi 8 sannan ayyukansa zasu kama kasa sosai - Sanata Ahmad Lawan

Yayi kira ga shugaba Muammadu Buhari da “Ya koma gida ya huta, don ya bawa kaninsa Ahmed Makarfi, damar jagorantar Najeriya ga cigaban da take bukata kamar yadda yayi a jihar Kaduna”.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel