Nigerian news All categories All tags
Boko Haram sun bunkasa ne saboda gwamnatin tarayya tayi bacci – Shehun Bama

Boko Haram sun bunkasa ne saboda gwamnatin tarayya tayi bacci – Shehun Bama

Shehun Bama dake jihar Borno, Shehu Kyari Ibn Umar El-Kanemi, ya bayyana cewa rashin kokarin gwamnatin tarayya wajen dakushe ayyukan Boko Haram na bayyana ne ya sa su bunkasa cikin sauri.

Ya ce hakan ne ya ba yan ta’addan isasshen dama wajen aiki, inda ya kara da cewa bunkasar yan ta’addan ya kasance gazawar jihar.

Da yake Magana a wajen taron gidauniyar Ejike Chukwu Educational Foundation a Etekwuru, Egbema dake karamar hukumar Ohaji Egbema na jihar Imo, Shehun wanda ya samu wakilcin tsohon shugaban ma’aikata na tarayya, Dr. Baba-kura Kaigama, yace “A lokacin gwamnatin tarayya da gwamnatin lokacin basu dauki abun da muhimmanci ba. Sun fara kokarin kama lamarin ne a lokacin da ya fara bunkasa. Shiyasa nace gazawar jihar ne.

Boko Haram sun bunkasa ne saboda gwamnatin tarayya tayi bacci – Shehun Bama

Boko Haram sun bunkasa ne saboda gwamnatin tarayya tayi bacci – Shehun Bama

Da yake bayyana cewa hawan shugaban kasa Muhammadu Buhari mulki ya sassauta ta’addancin, Shehun yayi korafin cewa akwai bukatar a kara kaimi sosai.

KU KARANTA KUMA: Tazarce: Ya kamata ka barwa matasa mulkin Najeriya – Kungiyar matasan Arewa ga Buhari

A halin da ake ciki, a ranar Litinin, 9 ga watan Afrilu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kudirinsa na son sake takara a 2019.

Hakan ya haddasa cece-kuce a kasar inda kowa ke tofa albarkacin bakin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel