Nigerian news All categories All tags
Wata daliba ta saki sakon muryar dake nuna wani Farfesa yana son kwanciya da ita kafin ta haye jarrabawar shi

Wata daliba ta saki sakon muryar dake nuna wani Farfesa yana son kwanciya da ita kafin ta haye jarrabawar shi

- A hirar da suka yi ta kusan minti shida, munji dalibar na rokon farfesan akan ya taimaka ya barta ta hanye jarrabawar shi, yayinda shi kuma dage da sai ya kwanta da ita har sau biyar kafin ta ya bata damar tsallake jarabawar tashi ko kuma yasa sai ta maimaita jarrabawar shekara mai zuwa

Wata daliba ta saki sakon muryar dake nuna wani Farfesa yana son kwanciya da ita kafin ta haye jarrabawar shi

Wata daliba ta saki sakon muryar dake nuna wani Farfesa yana son kwanciya da ita kafin ta haye jarrabawar shi

Majiyar mu Legit.ng ta samu wata hirar waya tsakanin wata daliba a jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke jihar Osun.

A hirar da suka yi ta kusan minti shida, munji dalibar na rokon farfesan akan ya taimaka ya barta ta hanye jarrabawar shi, yayinda shi kuma dage da sai ya kwanta da ita har sau biyar kafin ta ya bata damar tsallake jarabawar tashi ko kuma yasa sai ta maimaita jarrabawar shekara mai zuwa.

DUBA WANNAN: Mun zama abin dariya a idon duniya: Tsohon shugaban kasar Qatar yayi Allah wadai da nuna goyon bayan Isra'ila da Yariman Saudiyya yayi

Farfesan ya cigaba da tsorata dalibar da cewar tayi mishi karyar tana al'ada wanda kuma abun ba haka bane kawai ta fada ne saboda bata son kwanciya dashi. Farfesan ya kuma tambayar ta akan yanzu ta gama al'adar tata? sai ta ce mishi ta gama.

Majiyar mu Legit.ng bazata iya tabbatar da ingancin hirar ba amma kuma dalibar ta kira sunan Farfesan inda shi kuma cikin sauri ya ja kunnenta tare da yi mata gargadi akan da kada ta kara kiran sunan shi a duk lokacin da suke waya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel