Nigerian news All categories All tags
Shugaba Buhari ya bayyana dalilin sa na sake tsayawa takara

Shugaba Buhari ya bayyana dalilin sa na sake tsayawa takara

Sanarwar ranar Litinin din da ta gabata ta shugaban kasa Muhammadu Buhari na sake tsayawa takara a zaben 2019, zai kasance shine dan takara daya tilo na jam'iyyar APC.

Shugaba Buhari ya bayyana kudirin sa na sake tsayawa takara a wata ganawar sirrance da shugabannin jam'iyyar su a birnin tarayya kafin ya kama hanyar sa ta tafiya kasar Ingila domin halartar taron Commonwealth da kuma ganawa da Firai Ministar kasar, Theresa May.

Yake cewa, babban dalilin sa ya yanke shawarar sake neman takara ta kujerar shugaban kasa shine marari gami da muradin 'yan Najeriya dake ta yi ma sa kiranye akan aikata hakan.

Shugaba Buhari ya bayyana dalilin sa na sake tsayawa takara

Shugaba Buhari ya bayyana dalilin sa na sake tsayawa takara

A watan da ya gabata ne Kakakin shugaban kasa Mista Femi Adesina, ya shaidawa manema labarai na fadar Villa cewa, a halin yanzu lokaci ya yi wuri da shugaba Buhari zai bayyana ra'ayin sa na sake neman takara a zaben 2019.

KARANTA KUMA: Ashe Ruwan shan mu na Rijiyoyin Burtsatsai na iya gurɓata da kwayoyin cuta sama da 10m na Bahaya

Ya kara da cewa a wancan lokaci, muddin shugaba Buhari ya bayyana kudirin sa kafin shekara guda da gabatowar zabe zai baiwa 'yan adawa dama ta dagula duk wani shiri na Najeriya ta fuskar siyasa, zamantakewa da kuma tattalin arziki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel