Nigerian news All categories All tags
Da Buhari ya sani da bai ce zai kara tsayawa takara ba a 2019

Da Buhari ya sani da bai ce zai kara tsayawa takara ba a 2019

- Babu wani abin nunawa da gwamnatin Buhari tayi tun bayan hawansa

- Yakamata Shugaban kasa Buhari ya je gefe ya hutu

- Yan Najeriya kamata yayi su waye tahanyar zaben sabbin jini masu kishin kasa

Jam’iyyar CNPP ta ce, Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai kamata ya sake tsaya takara a 2019, a cewar jam’iyyar shugaban bai tabaku wani abun nunawa ba. Duk da cewa Muhammadu Buharin na da yancin tsayawa takarar amma idan akai la’akari da nasarorin da gwamnatinsa ta samu, to da kamata yayi ya je ya huta a gefe.

A jawabinsu game da batun sake tsayawa takarar na shugaba Buhari, ta hannun sakatarenta Chief Willy Ezugwu CNPP ta ce, yakamata yan Najeriya suyi karatun ta nutsu domin sake zaben sabon shugaba mai kishinsu, wanda ya san sha’anin tattalin arziki da kuma gudanar da gwamnati.

Da Buhari ya sani da bai ce zai kara tsayawa takara ba a 2019

Chief Willy Ezugwu

“Abin takaici ne yadda shugaban kasa yace zai sake tsayawa takara a karo na biyu, alhali rayuka da dukiyoyin mutane na cigaba da salwanta a kullum. Yanke shawarar sake tsayawa takarar da Shugaba Buhari yayi ba tare da wani kwakkwaran abin cigaba da za’a iya gani a nuna ba, abin takaici ne.” A cewar sakataren.

KU KARANTA: Wadanni na kokarin sanya takalman manyan mutane - Adesina

Kamar yadda muke gani a yau, batun yaki da cin-hancin da su keyi ya koma bata suna zalla da bita da kulli, domin da zarar ka koma APC shikenan zaka tsira kuma ka samu kariya duk kuwa da kayi sama da fadi da dukiyar kasa.” Shin wannan shine yaki da cin hancin da rashawa? Sakataren ya bayyana.

Ya kara da cewa, yan Najeriya yanzu, kamata yayi su bi sahun takwarorinsu na kasashen da suka cigaba ta hanyar zaben mutumin da yake kishinsu a matsayin shugaban kasa.

Kowanne shugaba da ya yake son a kara zabarsa, yana nuna irin aiyukan da yayi ne, amma sai dai kash ita wannan gwamnatin bata da wani abin da zata nuna, kama daga samar da aiyuka da sauran aiyukan cigaba duk bata yi ba.”

A saboda haka, “Mu yan Najeriya, mun ga abinda muka gani a tsawon shekaru ukun da su kayi, yunwa da karuwar rashin aiki ba zamu cigaba da jurewa ba, ba zamu kara zabar irin wannan gwamnatin ba a 2019.” CNNP ta jaddada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel