Nigerian news All categories All tags
Wadanni na kokarin sanya takalman manyan mutane - Adesina

Wadanni na kokarin sanya takalman manyan mutane - Adesina

- Adesina yace dama biyu yanzu ta rage tin da har Buhari ya bayyana kudirinsa na sake tsayawa takara, ko su tsaya kosu gudu

- Yace mai wuri yazo mai tabarma sai ya nade kayansa

- Adesina yace amma siyasa ce kowa nada damar tsayawa takara ba mai hanashi

Mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin sadarwa, Adesina yace dama biyu yanzu ta rage tin da har Buhari ya bayyana kudirinsa na sake tsayawa takara, ko su tsaya kosu gudu. Yace mai wuri yazo mai tabarma sai ya nade kayansa.

Adesina yace amma siyasa ce kowa nada damar tsayawa takara ba mai hanashi. Amma dai ni shawara ce nake bayarwa ga ‘yan takarar, wadda zasu iya dauka ko kin dauka. ‘Yan Najeriya dai sune zasu yanke wannan hukunci a shekara mai zuwa.

Wadanni na kokarin sanya takalman manyan mutane - Adesina

Wadanni na kokarin sanya takalman manyan mutane - Adesina

Duk da faduwar kudin danyen mai, amma mun samar da ingantacciyar wutar lantarki a kasar nan. Ga cigaba da aka samu ta fannin tattalin arziki, da kuma fannin noma a fadin kasar nan, inda muka mayar da fannin noma ya zamto na biyu a fannin arzikin kasar nan.

KU KARANTA KUMA: Tabbatar da tsayawar Buhari takara a zaben 2019 zai rufe bakin abokan adawa - Okorocha

“Yan Najeriya, shugaba Buhari ya sake dawowa neman takara, saboda haka mu tattara mu mara masa baya ko dan gaba da yaranmu da kuma wadanda ba’a ma kaiga haihuwa ba, mu sake zabarsa”, inji Adesina.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel