Nigerian news All categories All tags
Kungiyar kwadago na kasa ta bukaci karin albashi mafi karanci a Najeriya

Kungiyar kwadago na kasa ta bukaci karin albashi mafi karanci a Najeriya

- Sakatare Janar na kungiyar NLC, Peter Ozo-Eson ya ce kungiyar ta gabatar da sabon mafi karancin albashi da take bukata a taron da akayi a ranar 27 ga watan Maris

- Yace kungiyar tayi la'akari da halin da farashin abubuwa suke a kasar nan kafin suka fitar da sabon bukatar na karin mafi karancin albashi

- Ozo-Eson yace sabuwar bukatar na karin mafi karancin albashin hadin gwiwa ne tsakanin NLC da TUC

Kungiyar Kwadago na kasa (NLC) tace mafi karancin albashi na N56,000 da suka bukata a baya yayi kadan idan akayi la'akari da yanayin ta tattalin arzikin Najeriya ya sauya farashin abubuwa a kasuwanni.

Sakatare Janar na kungiyar NLC, Peter Ozo-Eson ne ya sanar da hakan yayin wata hira da yayi da kamfanin dillancin labarain (NAN) a babban birnin tarayya, Abuja a ranar Litinin 9 ga watan Afrilun 2018.

Kungiyar kwadago na kasa ta bukaci karin albashi mafi karanci a Najeriya

Kungiyar kwadago na kasa ta bukaci karin albashi mafi karanci a Najeriya

Ozo-Eson yace an gabatar da sabon bukatar karin mafi karancin albashin ne a taron kungiyar da akayi a ranar 27 ga watan Maris.

DUBA WANNAN: Yadda masarautar Saudiyya keyi da 'yan Shi'a a yau

Ya ce: "Mun dauki mataki lokacin da muka gabatarwa gwamnati bukatar mu ta farko kusan shekaru biyu da suka shude.

"Sai dai daga baya mun koma kwamitin bangarori uku kuma kwamitin ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki su gabatar da shawarwari.

"Sakamakon shwarwarin da aka bukata a bayar, wanda mukayi la'akari da halin da tattalin arzikin kasa ya haifar ga al'umma. Hakan yasa mukayi nazari kuma muka fitar da sabon albashin da mukaga ya dace da yanayin kasar a yanzu.

"Zamuyi tsayin daka a kan matsayar da muka cinma kuma muka mika zuwa ga kwamitin bangarori ukun amma a halin yanzu bazamu sanar da al'umma adadin albashin da muka tsayar ba."

Ya kuma ce kungiyar kwadago na kasa da kuma kungiyar masu sana'o'i (TUC) ne suka hada hannu guda wajen fitar da sabon albashin mafi karanci. Sakatare Janar ya bayyana cewa tun a baya kwamitin ya gabatar da bukatar karin albashin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel