Nigerian news All categories All tags
APC reshen jihar Kano ta sharwarci al'umma su guji jefawa PDP kuri'ar su a zaben 2019

APC reshen jihar Kano ta sharwarci al'umma su guji jefawa PDP kuri'ar su a zaben 2019

- Mataimakin Ciyamin din APC na jihar Kano, Alhaji Shehu Maigari, yace akwai dalilai masu yawa da zaisa yan Najeriya suki zaben PDP a zaben 2019

- Ya ce kura-kuren na PDP sunyi yawa saboda hakan yan Najeriya baza su iya mantawa ko yafe musu ba

- Mambobin jami'iyyar APC guda 2000 sun canja sheka zuwa PDP a Kano

Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta bukaci yan Najeriya su guji jefawa jam'iyyar PDP kuri'ar su a zabe mai zuwa a 2019. Mataimakin Ciyamin din jam'iyyar, Alhaji Shehu Maigari ya shaida wa jaridar Daily Trust a ranar Litinin 9 ga watan Afrilu cewa akwai dalilai da dama da sanya yan Najeriya baza su zabi PDP ba.

APC reshen jihar Kano ta sharwarci al'umma su guji jefawa PDP kuri'ar su

APC reshen jihar Kano ta sharwarci al'umma su guji jefawa PDP kuri'ar su

Shugaban jam'iyyar yace bayar da hakuri da shugaban PDP na kasa, Uche Secondus yayi cikin kwanakin nan da kuma kalaman da aka ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa inda yake cewa Allah ne ke hukunta PDP saboda zunuban da suka aikata kawai sun isa ishara ga yan Najeriya su kauracewa PDP.

DUBA WANNAN: Idan ba'ayi taron gangamin ba, Oyegun zai zarce a matsayin Ciyaman din APC - NEC

Maigari yace yan Najeriya su godewa Allah bisa yadda ya tilasta shugabanin guda biyu su fadiwa al'umma gaskiya. Yace abin alheri ne yadda mutanen da suka tafka kurakuren suna fitowa suna tuba da kansu.

"Ta yaya za'ayi mutane su kwashe shekaru 16 suna tafka kurakurai amma basu tasan ma ganewa ba sai bayan mulki ta kubuce daga hannun su? Idan da ace PDP sunyi nasarar cigaba da mulki a shekarar 2015, baza su taba gano kura-kuren ba kuma Najeriya zata cigaba da tabarbarewa.

"Mu dai a jam'iyyar APC na jihar Kano, munyi imani cewa jam'iyyar da tayi shekaru 16 tana tafka kura kurai bazata taba kawo wani gyara ba ko da kuwa an basu shekaru 60 suna mulki. Saboda haka, kura-kuren da jam'iyyar ta tafka sunyi muni da yawa kuma 'yan Najeriya baza su iya mantawa ko su yafe ba," inji shi.

Hakazalika, a kalla mutane 2000 ne suka canja sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP a jihar ta Kano. Jaridar Leadership ta ruwaito cewa canja shekar ya faru ne a karamar hukumar Sumaila dake jihar ta Kano inda tsohon gwamna Ibrahim Shekarau, Aminu Wali da Gambo Salau suka karbe su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel