Nigerian news All categories All tags
Yadda Sukari ke warkar da kekasassun Raunuka

Yadda Sukari ke warkar da kekasassun Raunuka

Cikin damuwar wani Mahaifi Moses Muradu, dangane da yadda wasu raunukan ke kekashewa magunguna, ya gudanar da bincike da ya nuna cewa wani abu mai rahusa kuma kewaye da mu zai iya taimakawa wajen warkar da raunuka kuma shine Sukari.

Murandu wanda babban malami ne a fannin nazarin kiwon lafiya a jami'ar Wolverhampton ta kasar Ingila, ya gano wannan bincike ne tun yayin da talauci ya masa katutu a tsibirai na mahaifar sa dake kasar Zimbabwe.

Wannan bincike ya sanya babbar cibiyar lafiya ta kasar Ingila ta dauke shi aiki tun a shekarar 1997, inda ya samu dama ta tabbatar da cewa babu wani sunadari mai warkar da raunuka cikin gaggawa tamkar Sukari.

Sukari

Sukari

A halin yanzu dai an tabbatar da wannan bincike na Murandu, inda aka wallafa shi a mujallar kulawa da rauni ta Journal of Wound Care a watan Maris na shekarar 2018.

KARANTA KUMA: 2019: Saraki sai ya fuskanci fushin Ubangiji muddin bai tsaya takara ba - Inji wani malamin addini

Legit.ng da sanadin jaridar Daily Trust ta fahimci cewa, wannan bincike zai taka rawar gani kwarai da aniyya a wasu sassan duniya inda mutane ke da karancin wadata ta sayen magunguna.

A cewar Murandu ga masu bukatar warkar da raunuka, "akan zuba Sukari ne kan raunin sai kuma a rufe shi da bandeji. Wannan kura-kuran na Sukari za su tsotse danshi da maikon raunin wanda dama suke baiwa kwayoyin cututtuka damar bunƙasa."

"A sakamakon rashin kwayoyin cututtukan Bacteria, rauni zai warke cikin gaggawa."

A halin yanzu dai, Murandu ya tabbatar da wannan bincike kan mutane 41 masu kekasassun raunuka da suka gaza jin magunguna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel