Nigerian news All categories All tags
Idan ba'ayi taron gangamin ba, Oyegun zai zarce a matsayin Ciyaman din APC - NEC

Idan ba'ayi taron gangamin ba, Oyegun zai zarce a matsayin Ciyaman din APC - NEC

Mun sami rahotanni cewa mambobin kwamitin zartarwa (NEC) na jam'iyyar APC ta amince da karin wa'adin mambobin kwamitin gudanarwa su cigaba da ayyukansu har na tsawon shekara daya nan gaba idan har jam'iyyar bata samu daman yin taron gangaminta ne shekara-shekara ba.

Mahukuntan sun cinma wannan matsaya ne a ranar Litinin a hedkwatar jam'iyyar da ke babban birnin tarayya Abuja, kuma hakan zai bawa Ciyaman din jam'iyyar Johb Odigie-Oyegun damar cigaba da kasancewa a kujerarsa har bayan zaben 2019.

Idan ba'ayi taron gangamin APC ba, Oyegun zai zarce a matsayin Ciyaman din APC - NEC

Idan ba'ayi taron gangamin APC ba, Oyegun zai zarce a matsayin Ciyaman din APC - NEC

"Idan har wasu dalilai sun sanya jam'iyyar ta gaza yin zabe ko taron gangami, abin da ya rage shine jam'iyyar ta amince da shawarar kwamitin zartarwa na 27 ga watan Fabrairun 2018 tunda hakan doka ya tanadar," kamar yadda bayanan da jaridar Premium Times ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Lalacewa: Nafi jin dadin saduwa da kananan yara - Wani mutum da ya yiwa karamar yarinya fyade

Rahotanni sun nuna cewa Ciyaman din jam'iyyar APC reshen jihar Ribas, Davies Ibiamu-Ikanya ne ya gabatar da bukatar amincewa da shawarwarin kuma Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya goyi baya kafin mambobin kwamitin zartarwa na jam'iyyar suka amince dashi.

A baya dama mambobin jam'iyyar sun amince da karin wa'adin na Oyegun da sauran yan kwamitin gudanarwan inda sukace zai takaita rikice-rikicen da ake samu a jam'iyyar amma daga baya akayi watsi da batun bayan shugaba Muhammadu Buhari ya nuna kin amincewarsa.

Wasu masu nazarin al'amuran siyasa na ganin cewa shugaba Muhammadu Buhari yayi hakan saboda ya dadada wa jigo a jam'iyyar ta APC, Ahmed Bola Tinubu wanda mutane suke ganin kamar yana son ya kori Mr. Odigie-Oyegun daga ofishinsa ne.

A halin yanzu dai ana ganin kamar Oyegun zai zarce a kan matsayinsa idan har ba'ayi taron gangamin ba duk da cewa akwai wasu 'yan jam'iyyar da suke ganin cewa ya zama dole ayi gangamin.

Wani mai fashin bakin siyasa a jam'iyyar APC, Ayo Akanji yace "Duk ruguntsimin da za'ayi babu dalilin da zai hana ayi taron gangamin" Inji shi. "A halin yanzu mutane sun fara siyan kayayaki don taron gangamin."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel