Nigerian news All categories All tags
"Tazarcen Buhari na nufin shugaban kasa dan kabilar Ibo a 2023"

"Tazarcen Buhari na nufin shugaban kasa dan kabilar Ibo a 2023"

Shugabannin jam'iyyar APC shiyyar kudu maso gabashin Najeriya a ranar Litinin din da ta gabata sun bayyana cewa tazarce nan da shugaba Muhammadu Buhari zai nema sune za su fi kowa cin gajiyar ta.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban jam'iyyar na shiyyar Cif Emma Eneukwu ta re da jami'in yada labaran jam'iyyar a shiyya Mista Hyacinth Ngwu suka sanyawa hannu a garin Enugu.

"Tazarcen Buhari na nufin shugaban kasa dan kabilar Ibo a 2023"

"Tazarcen Buhari na nufin shugaban kasa dan kabilar Ibo a 2023"

KU KARANTA: Mabambantan ra'ayoyi game da takarar Buhari a 2019

Legit.ng ta samu cewa yan kabilar ta Ibo dai a lissafin na su sun bayyana cewa zarcewar shugaba Buhari din ne kawai zai iya tabbatar da cikar burin su na fitar da shugaban kasa a Najeriya a shekarar 2023.

A wani labarin kuma, Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta People Democratic Party, PDP ta bayyana cewa batun kudurin sake tsayawa takara a zaben 2019 da shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana a ranar Litinin din da ta gabata matsalar sa ce da jam'iyyar sa ba ta su ba.

Haka zalika jam'iyyar ta ce har yanzu ita bai ishe ta kallo ba har sai shugaba Buhari din ya samu tikitin takarar a jam'iyyar sa sannan ne za ta maida martani amma ba yanzu ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel