Nigerian news All categories All tags
Tabbatar da tsayawar Buhari takara a zaben 2019 zai rufe bakin abokan adawa - Okorocha

Tabbatar da tsayawar Buhari takara a zaben 2019 zai rufe bakin abokan adawa - Okorocha

- Gwamnan jihar Imo Owelle Rochas Okorocha, yace bayyawar Muhammadu Buhari cewa zai tsaya takara a zabe mai zuwa zai rufe bakin abokan adawa

- Okorocha yace bayyanar zata kasancewa kamar amsa kiran ‘yan Najeriya ne ga cigaba da jagorancin kasar zuwa wasu shekaru hudu masu zuwa

- Okorocha yace Buhari yayi ayyukan kwarai saboda haka ya kamata a kara masa dama don cigaba da ire iren wadannanayyuka

Gwamnan jihar Imo Owelle Rochas Okorocha kuma ciyaman na kungiyar gwamnonin APC, yace bayyawar Muhammadu Buhari cewa zai tsaya takara a zabe mai zuwa zai rufe bakin abokan adawa.

Okorocha yace bayyanar zata kasancewa kamar amsa kiran ‘yan Najeriya ne ga cigaba da jagorancin kasar zuwa wasu shekaru hudu masu zuwa.

Tabbatar da tsayawar Buhari takara a zabe 2019 zai rufe bakin abokan adawa- Okorocha

Tabbatar da tsayawar Buhari takara a zabe 2019 zai rufe bakin abokan adawa- Okorocha

Okorocha a wani jawabi da ya fitar ta hannun sakataren labaru, Sam Onwuemeodo, yace Buhari yayi ayyukan kwarai saboda haka ya kamata a kara masa dama don cigaba da ire-iren wadannan ayyuka, kuma yace wadanda ke kokarin bata masa suna sai su nemi wani abunyi wanda yafi masu amfani a rayuwarsu.

KU KARANTA KUMA: Kamfanin MTN ta biya Najeriya Biliyan 165 cikin Biliyan 330 da ake bin ta

Ya kara da cewa shugaba Buhari sai yafi samun kuri’u a wannan zaben fiye da yanda ya samu a zaben da ya gabata na 2015; kuma za’a ida rusa abokan adawa da zarar an fara yakin neman zabe a fadin kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel