Nigerian news All categories All tags
Jami'an SARS sun kulle dan kasuwa a bandakin banki saboda ya ki yi masu alheri

Jami'an SARS sun kulle dan kasuwa a bandakin banki saboda ya ki yi masu alheri

A ranar Litinin ne wani dan kasuwa, Immanuel Ibe-Anyanwu, ya ja hankalin mutane a dandalin sada zumunta bayan ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Facebook inda ya ce yana kulle ne a bandakin bankin Zenith dake Ago Palace, a Okota dake jihar Legas.

Ibe-Anyanwu ya bayyana cewar wasu jami'an 'yan sanda na SARS ne suka kulle shi saboda ya ki yarda ya basu na goro.

Jami'an SARS sun kulle dan kasuwa a bandakin banki saboda ya ki yi masu alheri

Jami'an SARS sun kulle dan kasuwa a bandakin banki saboda ya ki yi masu alheri

Dan kasuwa, Ibe-Anyanwu; mai shekaru 37 ya kara da cewar jami'an sun kwace wasu takardun kamfaninsa tare da kwance masa lambar mota duk saboda ya hana su wani abu daga cikin kudin da ya karbo daga bankin.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga cikin kakin 'yan sanda sun kashe DPO

Labarin dan kasuwar ya samu yaduwa a dandalin sada zumunta na Facebook daga 'yan Najeriya domin nuna tausayi ga Ibe-Anyanwu da kuma neman a kawo masa taimako.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Legas SP Chike Oti ya ce sun gano jami'an da suka aikata hakan ga Ibe-Anyanwu kuma tuni hukumar ta bayar da umarnin kama su tare da gurfanar da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel