Nigerian news All categories All tags
Mabambantan ra'ayoyin jama'a game da kudirin sake tsayawar Buhari takara a 2019

Mabambantan ra'ayoyin jama'a game da kudirin sake tsayawar Buhari takara a 2019

A yayin da 'yan Najeriya ke cigaba da tofa albarkarcin bakinsu game da lamarin da ya mamaye kafofin yada labaran kasar a jiya na batun sake tsayawa takarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019, mun tattaro maku wasu daga ciki.

-'Yan Najeriya basu bukatar Buhari a yanzu - Fayose

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya bayyana cewa a halin yanzu kam, 'yan Najeriya matashi suke so mai jini a jika ba tsoho ba.

- Ka fadawa 'yan Najeriya nasarorin ka - Aka Ikenga

Mabambantan ra'ayoyin jama'a game da kudirin sake tsayawar Buhari takara a 2019

Mabambantan ra'ayoyin jama'a game da kudirin sake tsayawar Buhari takara a 2019

Shi kuwa shugaban wata kungiyar tsare-tsare da tunani mai inganci ta 'yan kabilar Ibo ya bukaci shugaban kasar ya zayyanawa 'yan Najeriya irin nasarorin da ya samu.

- Gwamnan Borno yayi murna

Shi kuwa Gwamnan jihar Borno dake a shiyyar arewa maso gabas nuna murnar sa yayi da samun labarin.

- Ai wannan ba labarin yadawa ba be - Makarfi

Da yake nasa tsokacin, tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon shugaban jam'iyyar ta PDP na rikon kwarya ya bayyana cewa ai wannan ko kusa ba ma labarin yadawa bane domin su daman haka suke tsammani.

- A jihar kuwa, matasa ne suka barke da murna

- Shugaba Buhari ya ki zabar ya bi tafarkin Mandela - Shehu Sani

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel