Nigerian news All categories All tags
Shugaban INEC ya nuna shakkun sa game da sahihancin zaben 2019

Shugaban INEC ya nuna shakkun sa game da sahihancin zaben 2019

Shugaban hukumar nan dake da alhakin shirya zabukan kasar Najeriya ta INEC watau Farfesa Mahmoud Yakubu ya bayyana shakkun sa game da yadda yace masu kutse ke neman gurbata sahihancin zabe mai zuwa a Najeriya na 2019.

Farfesa Mahmoud Yakubu ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabin sa wajen taron masu ruwa da tsaki na hukumomin zaben kasashen yammacin Afrika da aka gudanar a garin Abuja ranar Litinin din da ta gabata.

Shugaban INEC ya nuna shakkun sa game da sahihancin zaben 2019

Shugaban INEC ya nuna shakkun sa game da sahihancin zaben 2019

KU KARANTA: Gwamnan Kogi yayi alkawarin goyon bayan Buhari a 2019

A wani labarin kuma, Sabon kwamishinan zaben hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa na jihar Ondo Dakta Rufus Akeju ya bayyana cewa hukumar ta zabe watau Independent National Electoral Commission (INEC) tana nan ta na shirin kona dukkan katin zaben da ba'a karba ba kafin zaben 2019 mai zuwa.

Mista Akeju yayi wannan kwarmaton ne a yayin da yake fira da manema labarai a garin Akure, jiya Litinin inda ya bayyana cewa tuni da hukumar ta dukufa wajen ganin ta wayar wa da mutane kai don su je su anshi katin zaben su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel