Nigerian news All categories All tags
Jawabin Shugaban kasa Buhari a wajen taron Jam’iyyar APC na makon nan

Jawabin Shugaban kasa Buhari a wajen taron Jam’iyyar APC na makon nan

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi wani jawabi a taron Majalisar zartarwa watau NEC na Jam’iyyar APC mai mulki da aka gudanar a Birnin Tarayya Abuja. Mun tsakuro kadan daga abin da Shugaban ya fada daga Daily Trust.

A jawabin Shugaban kasar dai ya nuna cewa Jam’iyyar APC na iya bada lamuni ga Shugaban Jam’iyya John Oyegun da wasun su na sake neman takara idan su na bukata a zabe na gaba da za a shirya.

Jawabin Shugaban kasa Buhari a wajen taron Jam’iyyar APC jiya

Wani taro da Shugaban kasa Buhariya halarta na APC kwanaki

A jiya ne dai Shugaban kasar ya tabbatar da cewa zai tsaya takara a 2019. Ga dai jawabin da yayi kafin nan:

1. Ganin cewa a siyasa adadi ake dubawa, bai kamata APC ta raba kan ta ba don haka kar ayi sabanin da ya sabawa doka.

2. Dole APC ta gyara siyasar cikin gidan ta ta hanyar gudanar da zaben sababbin shugabannin Jam’iyya na kasa da Jihohi.

KU KARANTA: Mu na tare da Shugaba Buhari a zaben 2019 - Yahaya Bello

3. Shugabannin Jam’iyyan da ke rike da mukamai a halin yanzu za su iya fitowa takara idan har dokar Jam’iyya ta amince.

4. Dokar APC tace duk wanda ke neman wata kujera dole ya bar mukamin sa kafin zabe domin ganin an yi adalci a zaben.

5. Jam’iyya na iya yi wa wasu Shugabannin da su sake neman kujera a zabe na gaba afuwa muddin ba a sabawa ka’ida ba.

6. Za kuma a iya daga kafa ga sauran Shugabannin Jam’iyya da ke Jihohi ko Kananan Hukumomi da masu zuwa daga wasu Jam’iyyun.

7. A dalilin haka ya kamata Jam’iyya ta fitar da matsaya domin a san inda aka dosa

Shugaban kasar dai ya nuna cewa yana kan bakan sa na ganin John Oyegun da Majalisar sa sun tafi sannan kuma a gudanar da sabon zabe don haka dokar kasa da kuma tsarin Jam’iyyar APC ya shirya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel