Nigerian news All categories All tags
Babban bankin Najeriya yace ya kashe N5b akan harkar bunkasa noman shinkafa

Babban bankin Najeriya yace ya kashe N5b akan harkar bunkasa noman shinkafa

- Babban bankin Najeriya wato (CBN) ya ce ya kashe Naira Biliyan 55 akan bunkasa noman shinkafa, ta hanyar fito da tsarin bawa manoma bashi a cikin shekaru biyu da suka wuce a kasar nan

Babban bankin Najeriya yace ya kashe N5b akan harkar bunkasa noman shinkafa

Babban bankin Najeriya yace ya kashe N5b akan harkar bunkasa noman shinkafa

Babban bankin Najeriya wato (CBN) ya ce ya kashe Naira Biliyan 55 akan bunkasa noman shinkafa, ta hanyar fito da tsarin bawa manoma bashi a cikin shekaru biyu da suka wuce a kasar nan.

DUBA WANNAN: Kar wanda ya sake ya kara zaben jam'iyyar PDP

Daraktan babban bankin mai rikon kwarya a fannin sadarwa, Mista Isaac Okorafor, shine ya bayyana hakan a wani shiri da aka gabatar na tsarin bunkasa harkar kudade da kasuwanci, wanda aka gabatar a birnin Uyo dake jihar Akwa Ibom.

Ya ce shirin da babban bankin ya kawo an samu gagarumar Nasara, domin kuwa an samu karin ton miliyan 2.5, akan ton 2.5 da rabi da Najeriya take samarwa a da.

Ya ce bayan nasarar da babban bankin yake samu a harkar noman shinkafan, babban bankin ya kuduri aniyar fadada shirin bawa manoma bashin a shekarar 2018, ta hanyar samar da kayan aikin shinkafa, ta yadda za'a dinga samun karin ton 3.5 a karshen shekarar nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel