Nigerian news All categories All tags
Tallafin man fetur: Ministan mai Ibe Kachikwu yayi karin haske game da halin da ake ciki

Tallafin man fetur: Ministan mai Ibe Kachikwu yayi karin haske game da halin da ake ciki

- Gwamnatin Buhari tayi karin haske game da maganar tallafin man fetur

- Ministan mai Ibe Kachikwu yace NNPC ce kurum ta san nawa aka kashe

- Yanzu an yi ram da wasu da su ka cinye kudin tallafin man fetur a kasar

Karamin Ministan man fetur na kasar nan Ibe Kachikwu yayi watsi da labarin da ke yawo na cewa Gwamnatin Tarayya ta biya abin da ya haura Naira Tiriliyan 1.4 a matsayin tallafin man fetur a bana.

Tallafin man fetur: Ministan mai Ibe Kachikwu yayi karin haske game da halin da ake ciki

Karamin Ministan mai na Najeriya Dr. Emmanuel Ibe Kachikwu a ofis

Ministan kasar yayi jawabi a farkon makon nan ta bakin Darektan yada labaran Ma’aikatar Idang Alibi wanda ya zo hannun manema labarai. Ministan yace akwai bambanci tsakanin kudin da aka biya ‘yan kasuwa da kuma tallafin man fetur.

KU KARANTA:

Ibe Kachikwu ya kuma bayyana cewa kudin da ake biya yana fitowa ne daga hannun Hukumar NNPC na kasa. A dalilin cinye kudin tallafin man fetur dai an maka wasu manyan kasuwa George Ogbonna da Emmanuel Morah a gidan yari na shekaru 8.

Kachikwu yace NNPC kadai ta san makudan kudin da aka kashe daga asarar da aka yi wajen shigo da fetur domin kusan ita kadai ke jigilar mai. Ministan ya kuma yi kira da cewa ya kamata Najeriya ta fara neman wasu hanyoyin dabam da fetur yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel