Nigerian news All categories All tags
Kar wanda ya sake ya kara zaben jam'iyyar PDP

Kar wanda ya sake ya kara zaben jam'iyyar PDP

- Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Shehu Maigari, ya yi ikirarin cewar 'yan Najeriya suna da kwararan dalilai na kin zaben jam'iyyar PDP a zaben da yake gabatowa na shekarar 2019

Kar wanda ya sake ya kara zaben jam'iyyar PDP

Kar wanda ya sake ya kara zaben jam'iyyar PDP

Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Shehu Maigari, ya yi ikirarin cewar 'yan Najeriya suna da kwararan dalilai na kin zaben jam'iyyar PDP a zaben da yake gabatowa na shekarar 2019.

Mai gari ya shaidawa manema labarai cewar bayanin da tsohon gwamnan Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, yayi na cewa Allah yana hukunta 'yan jam'iyyar PDP ne saboda zunubansu, da kuma irin rokon da shugaban jam'iyyar ya dinga yi na kasa, Uche Secondus, hakan ya isa dalilan da zai saka 'yan Najeriya suki zabar jam'iyyar.

DUBA WANNAN: Duba kaga yawan littattafan da Shehu Dan Fodiyo ya rubuta

Ya ce 'yan Najeriya su godewa Allah da har ya kawo musu wadannan shugabannin biyun da suke bayyana musu gaskiya abinda yake faruwa, tunda sanadiyyar gaskiyar tasu ce yasa, da yawa daga cikin 'yan jam'iyyar suka fara furta laifukan da suka aikata.

"Ta ga yaya mutane zasu kwashe shekaru 16 suna aikata kuskure amma duk da haka su kasa ganewa har sai lokacin da damar su ta kwace? Inda ace jam'iyyar PDP ce ta sake lashe zabe a shekarar 2015, to tabbas haka zasu cigaba da aikata barnar su, kuma kasar zata cigaba da zama a cikin rikici da tashin hankali.

"Kamar yadda jam'iyyar PDP ta kwashe shekaru 16 tana mulkin kama karya, to koda za a barta ta sake shekaru 60 tana mulki tabbas zata cigaba da aikata kuskuren ne. Saboda haka, mulkin kama karya da jam'iyyar PDP ta yi a kasar nan ba abinda al'ummar Najeriya zasu mance dashi bane," inji shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel